Daga BASHIR ISAH
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa wa’adi da kuma takunkuman da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da ya auku a ƙasar, matakai ne da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta cim ma amma ba ra’ayin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ko Nijeriya ba.
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mr Ajuri Ngelale shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Talata.
Ngelale ya ce kuskure ne danganta matakan na ECOWAS da Shugaba Tinubu a matsayin shi kaɗai ko kuma da Nijeriya a matsayin ƙasa.
Ya ce “Dangane da wa’adin da aka bai wa sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar haƙƙi ne da ya rataya a wuyan ECOWAS amma ba Nijeriya ba.
“Kuma Ofishin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kasance shugaban ECOWAS, na jaddada yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke ƙoƙarin juya matsayar ECOWAS tamkar ta Tinubu da kuma ƙasarmu.
“Bisa wannan dalili ne Shugaban Ƙasa ya ga dacewar ya bayyana ƙarara cewar matakan da ECOWAS ta ɗauka, na ECOWAS ne amma ba nasa ba,” in ji Ngelale.