Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Abzinawa ƙabila ce da ke a yankunan Kudancin Afrika, musamman ma a ƙasashen kamar Nijar, inda yawansu ya kai kimanin 2,116,988, ƙasar Mali yawansu ya kai 536,557, Burkina Faso yawansu ya kai 370,738, sai ƙasar Aljeriya yawansu ya kai 25,000 sai kuma ƙasar Tunusiya inda yawansu ya kai kimanin 2,000.
Hakanan kuma ana samun wasu ’yan kaɗan a Faransa da koma Nijeriya. Abzinawa Bororo (Masu Yawo) ne kuma masu arziki. Akasarin Abzinawa sun kasance Musulmai ne.
Al’ummar Abzinawa na daga cikin ƙabilu da dama kamar Soninke, Mende, Bambara, Songhai, Madinka, Mossi da dai sauransu waɗanda suka taimaka wajen yin ciniki tsakanin ƙasashen sahara wanda ya haɗa dauloli na yammacin Afirka.