Ƙungiyar Igbo Women Assembly (IWA), wata ƙungiyar matan Ibo, ta caccaki gwamnatin jihar Legas bisa ƙudirin koyar da yaren Yarbanci kawai a makarantu na gwamnati.
Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta gurfanar da gwamnatin Babajide Sanwo-Olu a kotu kan wannan mataki.
Shugabar ƙungiyar, Nneka Chimezie, ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Umuahia ranar Alhamis.
IWA na da alaƙa da Ohanaeze Ndigbo, babbar ƙungiyar ƙabilar Ibo.
Chimezie ta bayyana damuwarta kan wannan doka a birni kamar Legas da ke da ƙabilu daban-daban.
“Ya kamata ne a koyar da Hausa, Igbo da Yarbanci a makarantu, ba wai a taƙaita kan yare guda kawai ba,” in ji ta.
Sai dai, shugabar ta jinjina wa Yarbawa bisa yadda suke kare yaren su.
Ta yi kira ga ‘yan Ibo su haɗa kai da IWA don hana yaren Igbo shiga cikin barazanar ɓacewa.
A cewarta, ƙungiyar za ta shirya biki don tunawa da ranar harshen uwa ta Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 21 ga Fabrairu a Umuahia, inda za a tattauna hanyoyin da za a kare harshen Ibo.
“Za mu gudanar da taron tattaunawa kuma mu fito da matsaya kan yadda za mu hana yarenmu ɓacewa,” in ji Chimezie.
Bugu da ƙari, ta yi kira ga Gwamna Charles Soludo da ya shawo kan ayyukan ƙungiyar Agunechemba, inda ta buƙaci a daina kashe matasa ba bisa ƙa’ida ba a Anambra.
“Idan an kama mutum, a miƙa shi ga ‘yan sanda don gudanar da bincike da shari’a, ba wai a kashe su ba,” in ji ta.