A ranar 13 ga watan Juni, 2023, ne aka rantsar da Majalisar Dokokin Tarayya ta 10 a Abuja, tare da zaɓen sabon Shugaban Majalisar Dattajai da Kakakin Majalisar Wakilai bayan fafatawa mai zafi a takarar waɗannan muƙamai.
A Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya samu nasarar lashe zaɓen zama shugaban majalisar inda ya kayar da abokin takararsa Abdul’Azizi Yari.
Nan ta ke kuma aka rantsar da shi. Sanata Ali Ndume na cikin waɗanda suka goyi bayan zaɓen Sanata Akpabio.
Hakazalika, Honarabul Tajudeen Abbas wanda shi ne zaɓin jamiyyar APC, ya zama Kakakin Majalisar Wakilai ta 10.
Majalisar Dokokin ta goma a Nijeriya, za ta cigaba da ayyukan kafa dokoki da bibiyar harkokin vangaren zartarwa a ƙasar.
Majalisar na ɗaya daga cikin ɓangarorin mulki uku da tsarin mulkin ƙasar ya samar, don tabbatar da rabon iko daidai da kuma taka wa juna burki, a inda wani vangare ke neman wuce gona da iri.
Muhimmin matsayin da Majalisar Tarayyar ke takawa a Nijeriya ne ya sanya ta zama ginshiqi wajen gudanar da harkokin duk wata gwamnati da kuma samun nasarar cika alƙawurra da manufofin da ta zo da su, ko kuma akasin haka.
Wasu ‘yan Nijeriya sun soki majalisar da ta shuɗe a kan abin da suka kira tsananin ba da haɗin kai ga vangaren zartarwa, inda suka yi zargin cewa hakan ya sanya ta kawar da kai ga wasu muradan al’umma da abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya.
Hakazalika, wasu masu ruwa da tsaki ciki har da su kansu ’yan majalisar sun nuna cewa majalisar ta yi fama da ɗimbin matsaloli ciki har da rashin bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa yadda ya kamata, da ƙarancin kuɗin gudanar da ayyuka da sauransu.
Wata muhimmiyar manufa ta mulkin dimokraɗiyya ita ce tabbatar da ganin an bai wa kowa dama domin ya shiga cikin harkokin gwamnati a dama da shi. Hakan zai tabbata ne a cewar ‘yan fafutuka ta hanyoyi da dama ciki har da ba da wakilci nagari.
Wajibi ne ‘yan majalisa ta goma su fahimci cewa su wakilai ne, su je zauren majalisar ne saboda jama’a sun zaɓe su don yin wakilci. Sun zo ne su gabatar wa gwamnati koke-koke da matsalolin mutane.
Shigar da al’umma cikin ayyukan majalisa ta yadda za a riƙa jin ra’ayoyinsu, abu ne mai matuƙar tasiri ga dokokin da za ta samar a tsarin dimokraɗiyya. Ya zamto ‘yan ƙasa an ba su dama su tofa albarkacin bakinsu cikin harkar tsara doka ko wata manufar gwamnati da za ta amfani ƙasa.
Wani babban aikin ‘yan Majalisar Dokoki shi ne samar da dokokin da za su taimaka wajen inganta rayuwa da tabbatar da cigaban ƙasa da kuma kawo sauqi ga al’umma. Akwai dokoki da yawa da ake sa ran gani ‘yan majalisar ta goma sun kawo a cikin shekara huɗu masu zuwa.
Halin ƙaƙa-ni-ka-yi da matsin rayuwar da ’yan Nijeriya suke ciki saboda gurvataccen shugabanci da kuma tsarin tattalin arziki da kuma ƙirƙire-ƙirƙire, wasu ɓangarori ne da ‘yan ƙasar za su zuba ido cikin gaggawa su ga an ɓullo da matakan rage musu raɗaɗi.
Dokokin ɓangaren tsaro ma, na cikin abubuwan da ke buƙatar a ƙarfafa su don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.
Batun ƙabilanci da addini na cikin manyan ƙalubalen da majalisa ta goma za ta fuskanta. Waɗannan al’amura sun yi ƙatutu a fagen siyasar Nijeriya, ta yadda suke tasiri a naɗe-naɗen shugabanci da rabon muƙamai. Matsalar ta yi ƙamari har a ɓangaren zartarwa da kuma a cikin majalisar dokokin ƙasar, inda aka fara kai ruwa rana game ɗan wane addini ne zai zama shugaban majalisar dattijai da kuma ta wakilai.
Hakazalika, wani abu da aka fi sukar majalisun tarayyar Nijeriya game da shi, shi ne zama ‘yan amshin shata. Majalisu ne da ba a cika jin suna taka burki ga ɓangaren zartarwa ba, kuma sukan gaza wajen nuna bijirewa ga duk wani aiki ko buƙata ko wata manufar gwamnati da mai yiwuwa za ta iya cin karo da muradun ‘yan ƙasar.
Wani muhimmin ƙalubale da ‘yan Nijeriya suke sa ran ganin canji daga majalisa ta goma shi ne inganta bibiya da bin diddigin ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Majalisun da suka gabata a Nijeriya sukan fuskanci suka bisa zargin gazawa wajen bibiyar ayyukan da ɓangaren zartarwa da kuma yadda suke kashe kuɗaɗe da majalisar ta keɓewa hukumomi da ma’aikatu.
Bugu da ƙari, wani ɓangare da ‘yan Nijeriya ke zuba ido su ga sauyi daga majalisa ta goma shi ne kan batun yaƙi da cin hanci da rashawa. Majalisar da ta wuce ta kafa tare da ƙarfafa wasu dokokin yaqi da cin hanci da rashawa, sai dai duk da haka ba a samu nasara sosai wajen aiki da dokokin ba.
Blueprint Manhaja na kira ga sabuwar majalisar ta dage wajen tabbatar da ganin ana bin dokokin da aka kafa matuƙar kuma ba haka ba, to da wuya a iya samun sauyin da ake buƙata.