Ƙa’idojin Azumin Ramadan

Daga RIDWAN SULAIMAN

Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai

‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, huɗubarmu ta yau za ta yi magana ne a kan ƙa’idojin da ke tattare da azumin Ramadan.

‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, yanzu abin da ya rage tsakaninmu da Ramadan wasu ‘yan kwanaki ne, don haka ya kamata mu tunatar da kawunanmu dangane da ƙa’idojin da Ramadan ke tattare da su domin samun tarin sakamako a watan da ke zuwa sau guda a shekara – wa ya sani ko wannan ya zama shi ne Ramadan na ƙarshe a wannan rayuwa!

An farlanta yin azumi ne a watan Sha’aban a cikin shekara ta biyu bayan Hijira. Azumin watan Ramadan ya tabbata ne da fadar Allah inda yake cewa: “Ya ku waɗanda kuka yi imani an sanya muku yin azumi kamar yadda aka sanya wa wadanda suka gabace ku ko kun zama nagartattu.” (Q 2:183)

Shi ma Annabi (SAW) ya bayyana azumi (a watan Ramdan) a matsayin ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci guda 5 da ake da su a cikin wani Hadisin Jibril wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito. Inda Mala’ika Jibril ya zo wa Ma’aikin Allah (SAW) a cikin sifar mutum ya yi masa tambaya game da Musulunci, yayin da Annabi (SAW) ya amsa da cewa: “Musulunci shi ne shaidawa babu abin da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzon Allah ne, sai Sallah, bada Zakka, azumin watan Ramadan da kuma zuwa aikin Hajji ga wanda ya samu iko.”

TAN-TANCE FARKON WATAN RAMADAN

Ana soma azumin Ramadan ne idan aka samu aukuwar ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu kamar haka: Ko ta ganin jinjirin watan Ramadan bayan faɗuwar rana a ranar 29 ga watan Sha’aban, ko kuma cika lissafin Sha’aban kwana 30 idan ba a ga jinjirin wata ba. Haka abin yake idan aka zo kammala azumin, za a ajiye azumin ne idan aka ga jinjirin watan Shawwal, idan kuwa haka bai samu ba to, sai a cika lissafin Ramdan ya zama 30.

An ruwaito Manzon Allah (SAW) na cewa: “Ku tashi da azumi idan kun ga wata, haka ma ku ci abinci idan kun ga wata. Amma idan wata ya faku (saboda hazo), sai ku cika kwanakin su zama 30.” [Imam Muslim]

WAƊANDA AZUMIN RAMADAN YA ZAMA WAJIBI A KANSU

Azumin watan Ramadan ɗaya ne daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da ake da su. Yin azumin wajibi ne a kan duk wani Musulmi balagagge mai hankali wanda ba ya cikin halin tafiya a lokacin azumin. Macen da ke cikin jinin haila ko nifasi, ba za ta yi azumi ba.

An ruwaito Manzon Allah (SAW) na cewa, “An gina Musulunci ne a kan shika-shikai guda biyar; da farko shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah kuma Muhammad Manzon Allah ne, sai sallah, bayar da zakka, ziyartar ɗakin Allah (Hajji) da kuma Azumin Ramadan.” [Bukhari da Muslim]

MUTANEN DA AKA ƊAUKE MUSU YIN AZUMI

Daga cikin mutanen da aka ɗauke musu yin azumi akwai; wanda ba shi da hankali, yaran da ba su kai shekarun balaga ba, tsofoffi masu yawan shekaru, da mai fama da rashin lafiyar da yin azumi a gare shi akwai haɗari ga rayuwarsa, irin waɗannan mutane ciyar da mabuƙaci kawai ake so su rika yi a duk ranar da suka sha azumi.

Mara lafiya da matafiyi suna da damar ajiye azumi. Fadar Allah SWT) a cikin Alƙur’ani Maigirma a Surah Al-Baƙara: “Amma idan ɗayanku ba shi da lafiya ko yana kan hanya, sai ya rama azumin da ya sha a gaba. Allah na son ku da sauƙi, ba Ya son ku da tsanani.” [Q2:184]

Haka nan, azumi ba ya zama wajibi a kan macen da ke haila ko nifasi (jinin haihuwa). Ba daidai ba ne su yi azumi a cikin wannan hali. Duk macen da ta sha azumi a wannan dalili (haila ko nifasi), sai ta rama azumin da ta sha a gaba bayan an fita daga Ramadan.

Ita ma mace mai ciki an yarda kada ta yi azumi muddin ta ji tsoron lafiyarta ko lafiyar abin da ke cikinta; haka mace mai shayarwa an dauke mata yin azumi da sharaɗin idan yin azumin zai haifar mata da damuwa ko ga dan da take shayarwa. Amma fa su biyun za su rama azumin duka adadin ranakun da suka sha. Idan rashin yin azumin nasu saboda tsoron lafiyar danta ne kawai, a nan baya ga rama azumin kwanakin da ta shayar za kuma ta ciyar daga abincin da aka fi amfani da shi a yankin.

SHARUƊƊAN RAMADAN

Akwai wasu sahruɗɗa guda biyu da ke sanya azumi ya zama karɓaɓɓe:

 • Niyyar Aazumi: Mai azumi ya yi niyya ingantacciya don yin azumi saboda Allah kowace rana kafin fitowar alfijir. Babu buƙatar sai ya furta niyyar tasa a fili, amma dole ya ƙudurta hakan a cikin zuciyarsa. Sai dai wasu malamai na ra’ayin cewa niyya daya ta ishi mutum a gaba daya watan babu buƙatar ya riƙa maimata niya kowace rana.
 • Sai kuma kamewa daga barin ci da sha da biyan buƙatar sha’awa da duka ayyukan da ka iya bata azumi, daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana da zummar bauta ga Allah.

ABUBUIWAN DA KE ƁATA AZUMI

Abubuwan da ke ɓata azumi iri biyu ne:
Ƙala’i (wannan rankon kwanakin da aka sha kawai ake buƙata), waɗannan kuwa su ne:

 • Faɗawar wani abu cikin uwar hanji ta baki, ko hanci, ko ido, ko kuma ta al’aura.
 • Rashin niyya (a azumin farali), ridda, ci da sha ko kwanciyar aure bisa tilastawa.
 • Jawo amai da ganagar.
 • Zuwan haila ko jinin haihuwa, ko da kuwa a kusa da faɗuwar rana ne.
 • Fitar da maniyi ko makamancin haka.
 • Ci ko sha, ko kuma saduwar aure bayan fitowar alfijir bisa rashin sanin cewa alfijir ya rigaya ya fito. Haka ma aikata kwatankwacin haka kafin faɗuwar rana bisa kuskuren cewa ai rana ta rigaya ta faɗi.

Kaffara, wannan rukuni kuwa, ba ranko kawai za a yi ba idan azumi ya lalace har da ƙarin kaffara. Abubuwan da ke ƙarƙashin wannan kuwa, sun haɗa da;
Ci ko sha ko biyan buƙatar sha’wa da gangar a lokacin azumi, wato daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Hukuncin aikata wannan shi ne ‘yanta bawa, ko yin azumi guda 60 a jere babu hutu. Idan kuwa wannan bai samu ba, sai a ciyar da mutum 60.

ABUBUBUWAN DA AKA YARDA A AIKATA LOKACIN AZUMIN RAMADAN

Abubuwan da aka yarda a aiakata su yayin azumin Ramadan su ne:

 • Yin wanka.
 • Shafa turare, diga maganin ciwon ido (idan ba za a ji dandanonsa a makogoro ba).
 • Yin allura ko gwada jini saboda dalili na rashin lafiya.
 • Yin asuwaki ko buroshi ko da kuwa da man goge baki kamar yadda wasu masana suka yi ra’ayi.
 • Kurkure baki da ruwa, amma ban da wuce gona da iri.
 • Ci ko shan wani abu da mantuwa. Wato mutum ya ci wani abu bisa mantuwar cewa ai yana azumi. Amma, dole ne a daina da zarar aka tuna.
 • Yin mafalkin jima’i da rana ba ya bata azumi.
 • Haka ma a wayi gari cikin janaba saboda jima’in ma’aurata bai bata azumi.
 • Macen da haila ya dauke mata cikin dare tana iya tashi da azuminta tun kafin ma ta yi wanka. Duka waɗannan, dole ne a yi wanka amma bai bata a zumi.
 • Amai wanda ba jayo shi da gangar aka yi ba.
 • Haɗiyar abun da babu makawa a hadiye shi, misali kamar mutum ya haɗiyi yawun bakinsa, ko kurar hanya, ko hayaki da makamantansu, duka ba su bata insha Allahu Ta’alah.

Godiya ta tabbata ga Allah.

Wannan huɗuba ce da aka gabatar a masallacin Juma’a na Nurul Yaqeen, Life Camp, Abuja, daga nakin Imam Ridwan Sulaiman – 02, Afrilu, 2021/19, Sha’aban, 1442

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*