Ƙalubale tsakanin malamai a tarihin addini a ƙasar Hausa

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kusan a iya cewa tun zamanin sahabbai, malamai ke gwabzawa a tsakanin su akan banbancin ra’ayi ko fahimta. Tarihin ilmi a addinin musulunci cike yake da irin waɗannan. Wasu ba su yi wani tasiri na ku zo ku gani ba, wasu kuma sun zama ma abin kwatance a wurin malamai. In muka yi la’akari da musayar ra’ayi tsakanin su Imam Malik da Imam Shafi’i akan wasu mas’aloli na addini. Ko tsakanin Maliku da Abu Ibrahim al Faƙihi a Madina, hatta ma acikin almajiran malikun an samu tsakanin shi da su. An sha samun banbancin fahimta tsakanin sa da Ibn Mahushuna, ko Suhnunu ko Ibn Habib da sauran su.

Da zamani ya fara nisa an samu irin wannan banbancin ra’ayi tsakanin al Hilli da Ibn Taimiyya. Haka kuma an samu irin wannan duk da ba su zauna tare ba, tsakanin Al Ghazzali da Ibn Rushd. A yayin da ya rubuta Tahfatul Falasifa, shi kuma Ibn Rush ya masa raddi da Tahfut al Tahfut.

Wannan bai tsaya ga malamai kawai ba, yakan faru ma tsakanin firƙoƙin addini. Misali a ɓangaren tauhidi akwai ‘yar tsama tsakanin Ash’ariyawa da Wahabiyawa. A yayin da su na farkon ke ganin Allah na ko ina, su kuwa Wahabiyawa suna ganin abin ba haka ya ke ba. Irin wannan saɓani ma ya taso akan ƙaddara, a tsakanin firƙoƙin musulunci da har ya haifar da Ƙadariyawa a addini.

Shigowar musulunci Ƙasar Hausa ma ya zo da ire iren waɗannan tun a farko farkon sa. Bamu da takamaiman ko an samu irin waɗannan sa toka-sa katsi a Daular Borno amma dai a Kano tun a ƙarni na 16 aka fara samun musayar yawu tsakanin malamai, mafi shahara ita ce wacce ta auku a tsakanin Sheikh Makluf Ali bin Salih al Bilbali da wani bajimin malami Bahillace, Sheikh Abdullahi Suka al Ba’awi.

Ba lokacin da za a iya tattaunawa akan wannan taƙaddama ta su, amma dai akwai alamun da ke nuni da a ƙarshe dai Abdullahi Suka wanda aka fi sani da Wali mai giginya ne ya cinye muhawarar. Labarin wannan shahararriyar muhawara ta wanzu har zuwa zamanin Danfodio, domin Muhamamdu Bello ya kawo bayanin ta a Infaƙul Maisur, har ma ya bayyana Shehu Suka da cewa, malami ne da Allah ya horewa kaifin harshe.

A farkon zuwa Shehu Usman Ɗanfodio ma wannan rigima ta taɓa kaurewa a tsakanin Shehu Usman da Malam Mustapha na Daura. Akan matsayin fitar mata wurin neman ilmi a addinin musulunci, hakan ne ya sanya Shehu ya rubuta Irshad al Ikhwan fi Kuruj an Niswan. A dai wannan lokaci aka ƙara samun wata muhawarar tsakanin malami da almajiran sa.

Sheikh Jibrin Ghaini wanda shi ne malamin Danfodio da qanin sa Abdullahi bin Fodio, ya yi ƙoƙarin ganin ya cusa tauhidin Zahiriyya acikin koyarwar addini, inda shi kuma Shehu da Abdullahi su ke ganin wannan sam ba daidai bane, a bar mutane akan tauhidin su na Ash’ari. Wannan ce ta sanya aka rubuta Shiga al Ghalil domin warware wannan mas’ala ga shi kuwa saboda tinƙaho da Shehu yake da Sheikh Jibrin a matsayin malamin sa har ya na cewa a wata waƙa “in an tambaye ka ni wane ne, ka ce ni taguwa ce acikin taguwoyin Jibrilu…” Jibrilu anan yana nufin malamin sa, Sheikh Jibrin Ghaini.

Jim kaɗan bayan mutuwar Shehu sai kuma ga rigimar gadon Shehu ta taso. A yayin da Bello ke ganin za a iya yin gado ta jini, kamar yadda ya bayyana a littafin sa Dhiya’ulil Amr, shi kuma Abdullahi sai ya ce masa wannan sam ba haka bane, ya rubuta wani littafi da ya kira, Al Ghayth al Wabl fi sirat Imam al adl. Wannan taƙaddama ta cigaba har zuwa wasu shekaru, sai bayan Yaƙin Kalambaina sannan suka shirya. Amma kuma har suka bar duniya ba wanda ya sakko daga kan ra’yin sa.

A wasu lokuta irin wannan banbancin ra’ayi da misayar yawu kan iya kaiwa ga yaƙe-yaƙe. Akan irin wannan ne ma ya haddasa rikicin tsakanin malaman Yandoto da masu jihadi. Kuma wannan rigima ce tun asali ta sanya aka kori Malam Sambo dan Ashafa daga garin Yandoto, wanda shi ne dalilin kafa Birnin Gusau da kuma dalilin da ya sanya da Fulani suka samu dama suka ƙone tsohon garin. Wani kyakkyawan misalin shi ne na rikicin da ya ɓarke tsakanin Sultan Bello da Malam Abdussalami. Koda yake ba rikici ne na ilmi ba, amma kuma ya faru ne tsakanin malamai biyu.

Shi dai Malam Abdussalami na cikin malamai Hausawa da suka bi Shehu Usman tun ma yana Degel. Kuma a dalilin sa ne su Shehu suka fara yin fito na fito da mayaƙan Gobir. Domin kuwa sun kama shi saboda a cewar su ya karya dokar hana yin wa’azi barkatai. Akan wannan kame ne ya buntsure musu har ta kai ga an ɗau makamai an buga a tsakanin Malam Abdussalami da almajiran sa da kuma dogarawan Sarkin Gobir a ɗaya ɓangaren, kuma cikin ikon Allah, ya yi musu ɓarna.

Ganin wannan varna da ya yi ta sanya ya gudu wurin malamin sa, Shehu Usman shi kuma ya bashi mafaka. Wannan mafaka ita ta hasala Sarkin Gobir Yunfa, kuma ita ta kunna wutar jihadin da ta lanƙwame Sarakunan Haɓe a Ƙasar Hausa.

Bayan rasuwar Shehu rikici ya kunno tsakanin Sarkin Musulmi Bello da Malam Abdussalami, a yayin da shi Abdussalami ke ganin ba a bashi abinda ya cancance shi ba a rabon ƙasa da aka yi, shi kuma Bello yake nuna masa ya yi gajen haƙuri. Wannan rikici na su na ƙunshe a cikin littafin Sultan Bello mai suna Sardal Kalam fi ma jara baini wa baina Abdussalam.

Wani rikicin da ya ƙara daukar hankali shi ne, wanda ya taso tsakanin Shehu El Kanemi da Sultan Bello dai, wanda ya taso a dalilin Jihadin da Fulani suka yi a Ƙasar Borno. An yi bajakolin hujjoji a wannan muhawara, kuma kowanne a cikin su ya bayar da na sa hujjojin akan abinda yake ganin shi ne daidai. Daga ƙarshe dai Sheikh Umar al Futi ne ya shiga tsakani ya kashe maganar.

Irin waɗannan suna nan jingim a cikin tarihi, wani lokacin tsakanin malami da malami, wani lokaci tsakanin mabiya, wani lokaci tsakanin makaranta da makaranta, kai wani lokaci ma tsakanin gari da gari.