Ƙalubalen da ke gaban Hausawa a ƙarni na 21

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ranar Alhamis da ta gabata ne 26 ga watan Agusta, wasu ƙungiyoyi da kafafen sadawar zamani daban-daban suka gudanar bikin ranar Hausa ta duniya, wanda ya kasance karo na biyu da aka shirya irin sa a bainar jama’a, saɓanin yadda aka faro shi kuma ya taqaita a shafukan sada zumunta, tun bayan da wani ɗan jarida ma’aikacin BBC Hausa mai suna Abdulbaki Jari ya ƙirƙiro da ita a shekarar 2015.

A shekarun baya babu irin wannan rana da za a ce al’ummar Hausawa sun ware suna tunatar da juna kyawawan al’adun su, gudunmawar da harshen Hausa ke bayarwa ga ci gaban rayuwa da sauran su. Kawai dai suna zaune ne kara zube, da taƙamar kasancewar su masu magana da babban harshe mafi saurin yaɗuwa a Nijeriya, kuma ɗaya daga cikin manyan harsunan Afrika.

Amma a gefe guda yaya manyan masu ilimi da manazarta daban daban da ake da su suka lura da ƙalubalen da al’ummar Hausawa da shi kansa harshen Hausa ke fuskanta, don samar da lokacin da ya dace a yi nazarin cigaban da harshen ya samar da matsalolin da yake cin karo da su, a jiya da yau.

Ina iya tunawa tun a shekarun baya wasu jami’o’i kan ware tsawon wasu kwanaki ana gudanar da tarukan qarawa juna sani, wanda ake kira da Makon Hausa, inda ake gabatar da laccoci da maqalu daga manyan masana. Kamar misalin Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato da Jami’ar Bayero da ke Kano, da sauran manyan cibiyoyin ilimi da ke da sashin nazarin harsuna.

Tun bayan da aka ƙirƙiro da bikin wannan rana kimanin shekaru biyar da suka gabata, bukin ya fi karkata ne a shafukan sada zumunta musamman ma shafin Twitter inda ake da gungun Hausawa ‘yan boko da masu ilimi da kishin ganin an samar da cigaba a vangarorin rayuwa daban-daban, da niyyar haɗa kai tsakanin masu magana da harshen Hausa da tunatar da su muhimmancin kiyaye al’adu da harshen Hausa.

A lokacin a kan mayar da ranar ta zama ranar amfani da Hausa wajen rubuce rubuce a shafin na Twitter, da tattaunawa kan wasu kalmomi na Hausa ko ma’anonin karin maganar Hausawa da azancin da ke ƙunshe a cikin su. Hakan yana taimakawa matasa ‘yan boko musamman waɗanda ke ganin amfani da Hausa wajen rubutu a shafukan sada zumunta ƙauyanci ne da rashin wayewa, babu ma kamar a manhajar Twitter. Hakan ya tilasta wasu da ba su yi zurfi a bokon ba su yi ta kokawa da turancin a ƙoƙarin ganin sun isar da saqon da suke son isarwa, ko don su ma a ɗauke su a cikin wayayyu.

Wannan ɗabi’a ta ‘yan Twitter ita ce ta rage masa karsashi a tsakanin matasan Arewa, abin da kuma ya ƙara bai wa Facebook karɓuwa sosai kenan, saboda yadda ya kasance tamkar jakar ɗan magori, ta ƙunshi kowanne irin mutum da ra’ayoyi iri daban-daban damar baje kolin sa.

Wannan ɗaya ne daga cikin ɗimbin matsalolin da harshen Hausa da al’ummar Hausawa ke fuskanta. Ba tun yau ba malaman mu da masharhanta ke kokawa da yadda ‘ya’yan Hausawa na asali ke nisanta kansu da harshen da al’adun su, waɗanda akasari tushen su daga addinin Musulunci ne, ko kuma addinin ne ya ƙara gyara su.

Da wuya ka ga ɗan boko bahaushe yana karanta littafin Hausa ko jaridar Hausa, ballantana waƙoƙin gargajiya na Hausa in ba waƙoƙin soyayya na zamani ba, ko da kuwa ka ganshi cikin sutura irin ta Hausawa, bai cika son nuna kansa a matsayin Bahaushe ba, sai idan hakan zai dace da wani burin sa ko ra’ayin sa. Wannan shi ya sa kasuwar jaridun Hausa ke ƙara baya, kasuwar adabin Hausa wacce a da ta yi shuhura, saboda haziƙan marubuta da suka riƙa fitar da rubuce rubuce da littattafai, yanzu ita ma ta mutu. Matasan marubuta da a yanzu suke tasowa a kafafen sada zumunta rashin gogewa da laƙantar harshen ya sa rubuce rubucen nasu ba sa samun tasirin da na baya suka yi.

Hatta shafukan watsa labarai da ake da su na Hausa a wasu kafafen sada zumunta, ba a cika ɗaukar su da muhimmanci ba, musamman daga ɓangaren hukumomi da manyan ‘yan siyasar Arewa da makamantansu, don haka babu abin da suke samu ballantana su inganta aikin ya kai darajar na turanci mallakin’ yan kudu.

Hajiya Mairo Muhammad Mudi, wata ‘yar jarida kuma marubuciya da ke da mallakin kamfanin jarida na Zuma Times ta tava koka min kan irin abin takaicin da masu shafukan labaru na Soshiyal Midiya suke fuskanta, inda take cewa, a qashin gaskiya, aikin jarida musamman na yanar gizo, yana ganin wulaƙanci da takaici. Babban ƙalubale shi ne na rashin kuxin tafiyarwa. Mutanen mu na Arewa da muka tsaya tsayin daka wajen kare martabarsu da karrama su ba sa ganin kimar abin da muke yi.

Manyanmu da ‘yan siyasarmu sun gwammace su kyautata wa ‘yan jaridun Kudu bisa ga na Arewa waɗanda in sun tashi cin mutuncin mu ba sa rabe ɗayan biyu kuɗin goro suke yi mana. Suna amfani da kafafensu wajen durƙusar da namu manyan da yankin mu na Arewa, amma kuma sune abin tallafawa. Mu sun raina mu sun fi basu daraja. Jaridun kudu na ci musu mutunci mu muna kare su, amma duk da haka su suke tallafawa, mu kuma ko oho, suna watsar da mu!

Bugu da ƙari, masu bibiya ba kowa ya ke da fahimta da tarbiyya ba, wasu da sun karanta labari in bai masu daɗi ba sai su yi ta aiko da kalamai na cin mutunci ko su danƙara muku ashar. Malam Bahaushe kenan!

A yayin da wasu qabilun ke shigowa Arewa suna cin abinci da samun alheri da harshen Hausa, mu namu ‘yan na gada qyamar harshen suke yi. Ta kai za ka je kamfanonin tallace tallace da kafafen watsa labarai ka ga wai ƙabilu ne suke gudanar abubuwan da ake yi da Hausa, ko kuma ka ga wanda ba bahaushe ba ne ke shugabantar sashin Hausa a wani babban gidan rediyo ko talabijin, kuma sai yadda ya ga dama ake yi.

Wani lokaci ka ji ana tallata wani kayan sayarwa da Hausa, amma kamar mutum ya yi amai. Ko ka ga allon talla a kan hanya an rubuta shi da wata bagwariyar Hausa. Duk kuma an zuba ido babu wata babbar murya da ke fitowa tana tsawatar wa.

Hatta a wasu manyan makarantu na duniya, inda ake koyar da harshen Hausa, sai ka je ka ga waɗanda ke koyar da Hausa qabilu ne da babu abin da ya haɗa su da harshen Hausa, in ba zaman wuri ɗaya ba. Mutum ya ziyarci ofisoshin jakadancin Nijeriya inda ake buƙatar masu tafinta da sauran ayyuka da suka danganci Hausa, sai ya zubar da ƙwalla.

A wata tattaunawa da muka yi da wani fitaccen masanin harshen Hausa, kuma shugaban ƙungiyar marubuta waƙoƙin Hausa, Farfesa Suleiman S. Mai Bazazzagiya ya shaida min cewa, harshen Hausa na daga cikin harsunan da suka fi saukin samar da damar ayyukan yi, musamman ayyukan da suka shafi koyarwa, aikin fassara, bankuna da sauran su, inda ake buƙatar wanda yake da wata shaidar karatu a Hausa, amma sai ka ga ƙalilan ne suke samun shiga.

A taƙaice, ina mai taya al’ummar Hausawa murna da samun wannan rana da za ta bayar da damar tattauna irin waƙannan ƙalubale da ba da shawarwarin yadda za a shawo kansu. Sannan kuma ya zama rana ce ta farkar da matasan Hausawa, da manyan jami’an gwamnati su gane cewa, kayan ado ba ya rufe katara!

Lallai ne sai mun darajanta kan mu a matsayin Hausawa da harshen mu na Hausa, kafin wasu su darajanta mu.