Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Tun daga ranar 11 ga watan Yuli na wannan shekarar, 2024 da Babbar Kotun ƙoli ta ƙasa ta yanke hukuncin ƙananan Hukumomi na da ‘yancin tafiyar da harkokinsu na mulki da sarrafa kason kuɗaɗen su na rabon arzikin ƙasa, jihohi da dama ke ta gaggawar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi saboda rashin tabbacin samun kuɗaɗen shiga daga Gwamnatin Tarayya da kuma cika wa’adin da aka basu na gama zaɓukan.
Sashi na bakwai sakin layi na ɗaya, na Kundi Tsarin Mulkin Nijeriya shi ya ba da damar kafa matakin gwamnati a ƙananan Hukumomi, wanda zaɓaɓɓun shugabanni ne kaɗai za su tafiyar da su. Sai dai kowacce jiha na da ‘yanci ta ƙayyade wa’adin da kowanne shugaban ƙaramar Hukuma zai yi, da kuma lokacin da ya dace a gudanar da zaɓe.
A yayin da wasu jihohin ƙasar nan irin su Ribas, Jigawa, Bauchi, Kogi, Filato, da Kaduna suka gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi don cika umarnin Kotun ƙoli, a wasu jihohin ƙura ce ta biyo baya, sakamakon zarge-zargen da ake yi wa hukumomin zaɓen jihohi na rashin yin kyakkyawan shiri kan zaɓukan, da nuna rashin ƙwarewa a wasu wuraren. Yayin da a mafi akasarin jihohin ake zargin an tafka maguɗi, inda ‘yan takarar da suka tsaya a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki a jihar sune suka lashe zaɓukan, in ban da ’yan tsirarun kujerun kansila da aka bar wa jam’iyyun adawa a wasu jihohin, kamar Filato.
Wata jaridar yanar gizo da ke fita kullum, Arewa A Yau, ta buga a babban labarinta na shafin farko na ranar Talata 22 ga watan Oktoba, bayan zaɓen da aka gudanar a Kaduna cewa, ‘Zaɓen ƙananan Hukumomin Jihar Kaduna: Fashi aka yi ba zaɓe ba -Jam’iyyar PDP’. Haka yake a sauran jihohin da aka gudanar da zaɓe, inda aka ce jam’iyya mai mulki ce ta lashe dukkan zaɓukan da aka yi, yayin da zargin maguɗi ko shirin za a yi maguɗi ke ta fita daga bakunan wakilan jam’iyyun adawa.
Sakamakon yadda kiraye-kiraye ke ƙara ƙarfi game gazawar hukumomin zaɓe na jihohi, wasu ‘yan siyasa na ganin kamata ya yi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta karɓi ragamar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi kawai, domin samar da ingantaccen zaɓe cikin tsari da zai zama karɓaɓɓe ga jama’a.
A daidai lokacin da nake wannan rubutun, wata Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano ta soke shugabancin Hukumar Zaɓe ta jihar, KANSIEC, sakamakon ƙarar da wani Aminu Aliyu Tiga da Jam’iyyar APC mai adawa reshen jihar suka shigar akan wasu shugabannin hukumar da suka zarga da kasancewarsu mambobin jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar, wanda hakan ya saɓawa dokokin da suka kafa hukumar zaɓe ta Jihar Kano. Wannan hukunci za a iya cewa ya dawo da hannun agogo baya, a yayin da bai wuce kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ba. Hakan kuma na zuwa ne bayan da aka rawaito cewa, tsohon tuɓaɓɓen shugaban hukumar zaɓen ya sanar da cewa, jam’iyyar adawa ta APC ba za ta shiga zaɓen da hukumar za ta gudanar ba, saboda rashin cika wasu sharuɗɗa. Yayin da kuma wasu rahotannin na daban ke cewa, kotun harwayau ta dakatar da hukumar zaɓe ta KANSIEC daga gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya za a gudanar a wannan Asabar ɗin.
A fili yake cewa, gwamnonin Nijeriya hankalinsu a tashe yake game da ɓamɓare ɓangaren ƙananan hukumomi daga ƙarƙashin ikonsu da aka yi, don haka suke yin duk mai yiwuwa domin ganin su ma sun ɓamɓari wani abu daga jikinsu. Babu mamaki ko shi ya sa a wasu rahotanni ke cewa, akwai gwamnonin da suka ƙulla wata yarjejeniyar sirri da shugabannin ƙananan hukumomi a jihohin da aka yi zaɓe, domin basu damar cigaba da kula da kuɗaɗen su da Gwamnatin Tarayya za ta turo, saɓanin hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke na bai wa ƙananan hukumomi 774 ’yancin cin gashin kansu.
A cewar majiyoyi, waɗannan yarjejeniyoyin sun haɗa da alƙawurran biyayya da yarjejeniyar ɓoye da nufin kaucewa umarnin raba kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomin. Sai dai da alamun ba lallai wannan shiri nasu ya yi tasiri ba, domin kuwa tuni wata guda bayan hukuncin Kotun ƙoli Gwamnatin Tarayya a ranar 20 ga watan Agusta, ta kafa kwamitin ma’aikatu mai mutane 10, ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, domin tabbatar da aiwatar da hukuncin.
A cikin jawabin da ya gabatar jim kaɗan bayan rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka ayyana cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe su duka, Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya bayyana rashin jin daɗinsa da hukuncin Kotun ƙoli, inda ya bayyana cewa a fahimtar sa wannan mataki ba shi ne abin da ya kamata ba, kuma ba lallai hakan ya haifar da ɗa mai ido ba. Kodayake ya yi wa sabbin shugabannin fatan alheri da gargaɗi kan su tabbatar sun yi wa talakawa abin da ya dace, da kuɗaɗen da za a tura musu.
Wannan dambarwa da ake tafkawa tsakanin ɓangaren gwamnoni da na ƙananan hukumomi na sake bayyana gaskiyar irin ɗimbin kuɗaɗen da aka daɗe ana cin ganimar su a ƙarƙashin kulawar gwamnoni, yayin da suke barin wasu ƙananan hukumomin da ƙyar suke iya biyan albashin ma’aikata. Babu mamaki shi ya sa a wasu jihohin ma Kantomomi kawai ake naɗawa babu wani batun zaɓe, domin gwamnati a matakin jiha ta samu damar cin karenta babu babbaka.
Wani tsohon shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Shehu Bala Usman, yankin da ya daɗe ƙarƙashin jagorancin shugaban riƙo, sakamakon fakewa da ake yi da yiwuwar samun rikici ko ƙalubalen tsaro, ya taɓa koka min cewa, kusan kowanne wata kafin a samu kuɗin da za a biya albashin ma’aikata, sai an haɗa da bashi da ‘yan dabaru na shugabanci kafin abubuwa su tafi daidai, saboda ɗan abin da ake bayarwa daga asusun gwamnatin jiha ba ya isar su.
Yanzu da wannan hukunci na Kotun ƙoli ya tilasta gwamnoni su gudanar da zaɓe, kuma a bai wa zaɓaɓɓun shugabannin damar jan ragamar yankunansu ba tare da yin katsalandan ɗin gwamnoni ba, ana sa ran ganin sabbin sauye-sauye a sabon tsarin tafiyar da shugabancin ƙananan hukumomi. Sannan ana sa ran ganin sabbin ayyukan raya karkara, gyaran magudanun ruwa da hanyoyi, inganta tsarin ƙananan asibitoci da makarantun firamare, kyautata albashin malamai da sauran ma’aikata. Bunƙasa harkokin noma da samar da wutar lantarki a ƙauyuka, da kuma tallafawa mata da matasa da sana’o’in dogaro da kai, don rage illar zaman kashe wando ga matasa, da yaƙi da aikata laifuka.
Da fatan sabbin zaɓaɓɓun shugabannin za su yi abin da ya dace wajen sauke nauyin al’ummar da suka zaɓe su, musamman a wannan lokaci da mafi yawan ‘yan Nijeriya ke fama da matsin rayuwa, da yunwa, Da fatan za su ba mara ɗa kunya, su riƙe amanar da aka basu, su guji facaka da yin almubazzaranci da dukiyar al’umma, su kawo sauyin da za a daɗe ana tunawa da su.