Ƙalubalen da sabon Shugaba Ƙasa Bola Tinubu zai fuskanta

Ana yawan bayyana Nijeriya a matsayin uwa ma ba da mama a Afirka saboda yawan al’ummarta da kuma ƙarfin tattalin arzikinta sai dai tana fama da wasu gagaruman matsaloli – da za su tunkari Bola Tinubu yayin da yake shirin karvar mulki ranar Litinin.

Ba lalle bane Tinubu mai shekara 71 ya damu da ƙalubalen. A matsayinsa na wanda ya jagoranci jihar Legas a matsayin gwamna sau biyu, ya farfaɗo da cibiyar kasuwancin ta Nijeriya – wani lamari marar sauƙi kuma ya san da batutuwan.

Sai dai ‘yan Nijeriya, da waɗanda ma ba su jefa masa ƙuri’a ba, za su so su ga sauyi cikin hanzari daga Tinubu. Ga wasu daga cikin manyan ƙalubalen da zai fuskanta da ma yadda wataƙila zai warware su.

Wannan ƙalubale ne da gwamnatocin baya suka yi saurin sauyawa tun bayan da aka ƙaddamar da shi a shekarun 1970.

Duk da kasancewar Nijeriya na da arzikin man fetur, ƙasar ta ƙasa tace danyen manta domin biyan buƙatun ƙasa a don haka take shigo da albarkatun man fetur waɗanda kuma ake sayarwa kan farashin da gwamnati ta ƙayyade. Kasancewar akasari farashin yana ƙasa da farashin da ake shigo da shi, sai gwamnati ta riƙa biyan tallafin.

Amma tallafin yana shafar harkokin kuɗi na gwamnati. A shekarar da ta gabata, gwamnatin ta kashe naira triliyan 4.3 kwatankwacin dala 9.3 kan tallafin mai sannan cikin wata shida na wannan shekara, an ware naira triliyan 3.36 domin wannan bangare.

Kuɗaɗen da ake biya na shafar ayyukan gina al’umma kamar makarantu da asibitoci amma cire tallafin ba zai zo da sauqi ba saboda zai janyo hauhawar farashin kayayyaki.

Yunƙuri na ƙarshe da aka yi a 2012ya janyo zanga-zangar gama-gari.

Yan Nijeriya da dama da suke cikin ƙalubale da suka saba ganin yan siyasa na sama da fadi da arzikin ƙasar, suna ganin samar da man fetur a farashi mai sauƙi shi ne hanyar da za su amfana daga arzikin aasar.

Sai dai Tinubu ya sha nanata cewa ya zama dole a janye tallafin mai kuma makusantansa sun dage cewa yana da ƙudirin yin hakan.

Kashi 37 cikin 100 na masu zaɓe ne kawai suka zaɓi Tinubu, wanda hakan ya sa ya zama zaɓaɓɓen shugaban Nijeriya da yake da mafi ƙarancin quri’u tun 1999.

Ya yi nasara a zaɓen mai zafi wanda ya fito da rarrabuwar kai ta fuskar addini da ƙabilanci a fili.

Dole ne ya zama ya yi aiki wajen daidaita al’amura game da zavin ‘yan majalisarsa domin ɗinke barakar da aka samu.

Akwai alamu da ke nuna cewar ya soma yin hakan inda rahotanni ke cewa ya gana da ’yan siyasa biyu daga ɓangaren hamayya tun bayan da ya lashe zaɓen na watan Fabarairu.

Rabiu Musa Kwankwaso, babban abokin hamayyarsa daga arewacin Nijeriya wanda kuma ya zo na huɗu a zaɓen da aka yi.

Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers mai barin gado kuma mai ƙarfin faɗa aji.

A matsayin gwamnan Legas, wataƙila Tinubu a iya cewa shi ne yake da mutane daga ƙabilu daban-daban cikin jerin ’yan majalisarsa inda ya naɗa mutanen da ba yan asalin Legas ba kan muƙamai muhimmai, wanda har yanzu, ba kasafai ake samun haka ba.

Akasarin mutane sun amince cewa a matsayinsa na kwararren akanta, wani fanni da Tinubu ya kware a kai – amma abubuwa ba su tava yi wa ‘yan Nijeriya muni ba:

Mutum ɗaya cikin uku ba su da aikin yi.

Hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 22 cikin 100.

Mutum miliyan 96 ba sa iya kashe dala 1.90 kowace rana.

Yawan arzikin da Nijeriya ke samarwa ya kai dala 2,065 a 2021 idan aka kwatanta da dala 70,248 a Amurka da dala 46,510 a Birtaniya.

Ƙarancin kuɗaɗen shiga sakamakon faɗuwar farashin mai.

Mista Oyetade ya ce, alƙaluman sun banbanta sosai da abin da ya tarar a Legas cikin 1999.

Wannan na iya zama an kambama amma yadda Tinubu ya yi amfani da fasaha wajen inganta haraji a Legas da havaka kuɗaɗen shiga da fiye da kashi 400 cikin 100 a shekara takwas.

Tinubu zai so kamo bakin zaren wannan matsala cikin sauri, la’akari da girman matsalar. Gwamnatinsa za ta tunkari yan bindiga a arewa maso yamma da matsalar sace-sacen mutane a faɗin ƙasar da rikicin ƙungiyar da ke neman ballewa daga kasar da ke kudu maso gabas. Da munanan rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma da ke ci gaba da gudana a jihohin da ke tsakiyar ƙasar.

A lokacin yakin zaɓe, mataimakin Tinubu, Kashi Shettima da ke jiran gado, ya ce zai yi amfani da kwarewarsa a matsayin gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabas mai fama da rikicin ’yan bindiga da Boko Haram.

Amma ƙalubalen tsaro sun sake dawowa tun bayan da bar ofis a 2019 sannan Shugaba Buhari, tsohon janar na soja, ya gaza samar da maslaha a tsawon shekara takwas da ya yi kan mulki – a maimakon haka, matsalar tsaron ta ta’azzara a faɗin ƙasar.

Manufar Tinubu da Shettima ta haɗa da yaƙar ayyukan ta’addanci inda sojoji na musamman za su fatattaki masu garkuwa da masu tsattsauran ra’ayi.

Mafi muhimmanci shi ne, sun bayar da shawarar janye jami’an ’yan sanda daga zama dogaran fitattun mutane lamarin da zai sa a ga ƙarin ’yan sanda kan tituna don yaqar laifuka.

Tun bayan zaɓen, ya yi bulaguro zuwa ƙasar waje sau biyu, abin da ya janyo tambayoyi game da lafiyarsa. A 2021, ya shafe watanni a London ana kula da lafiyarsa sai dai ba a bayyana cutar da ke damunsa ba.

Ya yi watsi da sukar da ake inda ya ce aikin na shugaban ƙasa ba ya buƙatar lafiyar mai wasan tsere kuma makusantansa sun shaida wa mutane cewa Shugaban Amurka, Joe Biden ya fi shi shekaru – 80.

Amma ’yan Nijeriya sun gaji da ganin yadda shugabanni suke shafe lokaci a ƙasashen waje don kula da lafiya lamarin da ya sa gwamnati ke rikici kan madafun iko. Wannan ya faru a qarqashn Buhari da Umaru Musa Yar’adua wanda ya rasu a 2010.

Sun kuma damu da irin cece-kucen da ke biyo baya. Kafin a yi zave, Tinubu ya musanta zarge-zargen alakarsa da miyagun ƙwayoyi da rashawa.

Tun nasararsa, an bankaɗo cewa ya tava riqe takardar fasfo ɗin Guinea wanda bai saba doka ba amma dai ba a taba bayyana haka a baya ba.

Wassalm. Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *