Ƙalubalen rayuwar ɗalibai a makarantu abin dubawa ne

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani labari da ya ɗauki hankalin ’yan Nijeriya sosai cikin makon da ya gabata shi ne labarin kisan gillar da wani malamin makaranta a Jihar Kano ya yi wa wata ƙaramar ɗaliba mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar, bayan tsawon wata guda da ya yi yana garkuwa da ita, don jiran kuɗin fansa har Naira Miliyan 6 daga iyayenta.

Wannan yana zuwa ne ba da jimawa ba, bayan wani kisan gillar da aka yi wa wani ɗalibi ɗan makarantar sakandire a Jihar Legas mai shekaru 12 mai suna Sylvester Oromoni, wanda wasu abokan karatun sa suka azabtar da shi har ya rasa ransa.

Kafin wannan, wasu matsalolin irin wannan sun faru a makarantu daban-daban, sakamakon sakacin malamai ko shugabannin makaranta, iyaye ko mutanen gari da ke maƙwaftaka da makarantar, waɗanda su ma suke da alhakin sa ido da kula da abubuwan da ke kai wa da komowa a makarantun da ke maƙwaftaka da su.

Kusan a kowacce rana a Nijeriya sai an fuskanci wata matsala ko ƙalubale da ya shafi lamarin gudanarwar wata makaranta, walau ta gwamnati ko ta masu zaman kansu, da ta shafi harkar tafiyar da makarantar, gudanar da sha’anin malamai, biyan albashi, da ƙalubalen tafiyar da harkokin ɗalibai. Ko kuma uwa uba, sace ɗalibai da yin garkuwa da su, har sai an biya kuɗin fansa, wanda yanzu shi ya fi tasiri da haifar da damuwa.

Iyaye da dama ba ni kaɗai ba, suna shiga matsananciyar damuwa a duk lokacin da aka ce yaran su za su tafi makaranta, a matakin firamare ne ko na sakandire? Makarantar kwana ce ko ta jeka ka dawo? Saboda fargabar ko wanne hali za su samu kansu a ciki. Ko dai su dawo a raye cikin walwala da ƙoshin lafiya ko kuma su dawo a galabaice cikin gajiya ko da jikkata, wacce aka samu daga wajen ƙwallo ko ƙiriniya. Wani lokaci kuma sakamakon cin zali daga abokan karatu ko waɗanda suke ajin gaba, ko ma malamai.

Sau da dama ana kuka da yadda wasu malamai ke amfani da damar da suke da ita ta tarbiyya da tsawatar wa wajen yi wa wasu daga cikin ɗaliban su horo mai tsanani har ya kai ga illata su ko yi musu mugun rauni a jiki. Wani lokaci kuma damuwar daga yanayin iya riƙon fushi ko ɓacin rai ne daga malamin, don wata matsala da yake ciki ta rayuwa, sai ta sa shi yin hukunci cikin fushi, a ƙarshe ma har da yin lahani ko kuma a samu tsautsayi.

A wasu lokacin rashin jin daga wajen yaran ne, domin kuwa sau da dama yaro zai bar gida a matsayin salihi, amma da zarar ya bar gida sai ya juya ya zama ifritu, sai ya buwayi kowa a makaranta, saboda rashin jin magana, da rashin mayar da hankali a karatu, duk kuwa da ƙoƙarin da iyaye suke yi a kansa, a gida da makaranta, da gudunmawar da malamai ke bayarwa.

Amma babban abin tashin hankali ga iyaye da masu makarantu shi ne a ce yaro ya tafi makaranta, amma bai dawo ba! Ko dai ya ɓace a hanya ko vatagari sun sace shi za su karɓi kuɗin fansa, ko kuma mafi muni shi ne a ce yaro ya ɓata ba a sake jin ɗuriyarsa ba. Kamar yadda yake faruwa a wasu lokuta da dama.

Batun satar yara ’yan makaranta, musamman ’yan mata, da yake faruwa a wasu yankuna na arewacin ƙasar nan inda ake yawan samun rahotannin satar ’yan makaranta akai-akai. Yayin da ake shigar da su cikin dazuka, a tagayyare, ga yunwa ga duka da wulaƙanci, cikin rana, ruwa da iska. Wasu marasa imanin ma har fyaɗe suke yi wa ’yan matan da suke kamawa.

Labarin abin da ya faru a Legas da Kano ya girgiza ’yan Nijeriya sosai, kuma ya jefa su cikin fargaba da damuwa kan makomar yara a makaranta. Matsalolin kullum ƙaruwa suke yi, rashin tsaro, rashin yarda da rashin kulawa, sun fara yin yawa a akasarin makarantun da muke tura yaran mu. Rashin aminci da zargi ya fara shiga zuciyoyin wasu iyayen a game da malaman da ke koyar da yaran su ko makarantun da suke zuwa.

Abin takaici ne matuƙa, a ce shugaban makaranta ko malamin da aka bai wa amanar kula da ilimantarwa da tarbiyyantar da yara, shi ne zai ƙulla makircin yadda za a sace ɗaliba mai ƙarancin shekaru, har a yi garkuwa da ita tsawon kwanaki, don kwaɗayi da zarmewar zuciya, da tunanin tara abin duniya ba tare da wahala ba. A ƙarshe kuma har ya sanya mata guba a abin sha ta mutu.

Makamancin haka ma an ce ya faru a Zariya da ke Jihar Kaduna, inda aka zargi wani malami da shirya irin haka, kuma a ƙarshe ya kashe ɗalibar bayan da ya lura ta gane shi.

Har yaushe hukumomi, jami’an tsaro da iyayen yara za su cigaba da naɗe hannu suna ganin ɓata-gari da ke sajewa cikin aikin malanta, aiki mai daraja da martaba, suna aikata munanan ayyuka kan yara ƙanana da ba su ji ba, ba su gani ba? Ya kamata gwamnati da masu makarantu su ƙara sa ido da gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan duk wani malami da ya nemi a ɗauke shi aikin koyarwa, a binciki lafiyar ƙwaƙwalwarsa a kuma binciki ayyukansa na baya, har da abokan sa da halayyar sa ta gida.

Lallai ne a samar da ingantaccen tsaro a makarantu, musamman makarantun kwana da ke ƙauyuka da bayan gari. Ba wai a ajiye ’yan sanda biyu ko uku, waɗanda ko su ba za su iya kare kansu ba. A girke jami’an tsaron da suka dace da makaman da suka kamata, domin ko ganin su ma ya iya hana aikata wani mummunan abu ba. Sannan kuma kasancewar su a kusa zai iya taimakawa wajen kai ɗaukin gaggawa, don kare aikata wani abin da bai dace ba.

Lallai ne ƙungiyar malaman makarantu ta fitar da wani tsari na tantance baragurbi daga cikin su, da kuma gudanar da tarukan bita akai- akai ana koyar da su sabbin dabarun koyarwa da kula da yara a makaranta. Don a kaucewa, samun aukuwar halayen da ba su kamata ba, a sanadiyyar shaƙuwar ɗalibai da malamai.

A riƙa sa ido da kiyaye duk wata ƙofa da aka lura za ta iya zama barazana ko sanadin aukuwar wata ɓarna a tsakanin malamai da ɗalibai. Sau da dama an sha samun rahotannin inda malami ya yi wa ɗalibarsa fyaɗe, ko ya ci zarafin ta ko kuma ya yi lalata da ita har ta samu ciki, wanda a dalilin haka kuma ya gurguntar ma ta da karatun da ta ke yi.

Abin kunya ne a ce malami da yake zaman mai raino da tarbiyya, shi ne kuma zai zama ummulhaba’isin lalacewar rayuwa ko salwantar da ran ɗalibarsa, wanda aka ba shi alhakin koyar da ita da kula da amanar ta. Ta yaya za a ce malami zai riqa soyayya da ɗaliba a cikin makaranta, ko mai zai sa malami ya riƙa yi wa ɗalibansa mata ko maza mu’amalar da ba ta kamata ba, wanda ya saɓa da tarbiyya da ƙa’idojin koyarwa.

Sannan kuma, akwai babban nauyi a kan mutanen anguwa da maƙwaftan makaranta, su kwafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin shugabannin makaranta, malamai da iyayen yara, har da wakilan ɗaliban, domin tattauna matsalolin makaranta da rayuwar ɗalibai. Hakan zai taimaka wajen gano matsala da saurin shawo kanta.

Ya kamata dai abin da ya faru a Kano ya zama ishara ga malamai da sauran mutane masu zarmewar zuciya da ke tunanin aikata wani mummunan abu makamancin wannan su canja tunani a kai, domin dai ga abin da duniya ta shaida faruwarsa, inda kowa ke tir da Allah tsine da waɗanda suka haɗa baki da aikata wannan ɗanyen aiki.

Ya Allah ka nufe mu da aikin da na sani. Ka tsare zuciyar mu daga mugun nufi da ƙetare iyaka. Ka sanya wa zuciyar mu wadata da ƙalilan ɗin da muke da shi, ka sa masa albarka da mu baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *