Ƙananan hukumomi 8 sun gabatar da sakamakon zaɓen gwamna a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ya zuwa yanzu ƙananan hukumomi takwas daga cikin 23 ne suka gabatar da sakamakon zaɓukkansu.

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Binji wanda APC ta samu ƙuri’u dubu 13,410 yayin da PDP ke biye mata da ƙuri’u 11,078, sai kuma ƙaramar hukumar Wurno inda APC ke da ƙuri’u 17,350 sannan PDP na da 13,099.

Sai kuma ƙaramar hukumar Yabo da jamiyyar APC ta samu ƙuri’u 14,729 inda PDP ta tashi da ƙuri’u 12,014.

Haka lamarin yake a ƙaramar hukumar Isa, inda ɗan takarar APC, Ahmad Aliyu, ya doke abokin karawarsa Malam Saidu Umar da ƙuri’u 13,632, Malam kuwa ya tsira da ƙuri’u 15,117.

Yayin da sakamakon karamar hukumar Gwadabawa ya nunar da cewa jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 19,036, PDP kuwa 16,652.

Karamar hukumar Rabah ita ce ta shida wajen gabatar da sakamakon zaɓen, jami’in tattara sakamakon ya ce APC ta samu ƙuri’u 12,759, PDP ta samu 11,120.

A ƙaramar hukumar Tureta sakamakon ya nunar PDP ta samu ƙuri’u 10, 025, yayin da APC ta samu 9, 831.

Sai kuma Bodinga inda jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 18,986 yayin da PDP ke da ƙuri’u 16,440.