Ƙananan hukumomi a Jihar Katsina sun fara cin gashin kansu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Muƙaddashin Shugaban ƙungiyar Shugabannin ƙananan Hukumomi ta ƙasa (ALGON) a reshen jihar Katsina, Rabo Tambaya ɗanja, ya yaba wa gwamnatin Dikko Umaru Raɗɗa kan tabbatar da bai wa ƙananan hukumomi ‘yancinsu na sarrafa kuɗaɗensu ba tare da wata katsalanda ba a jihar.

ɗanja ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin a ƙaramar Hukumar Danja wanda ya ce saɓanin sauran jihohi da ke ƙorafi game da katsalandan gwamnoninsu kan kuɗaɗensu, jihar Katsina ta zama ta daban wajen baje komai a faifai tare da tabbatar da matakin bai wa ƙananan hukumomin ‘yancinsu kamar yadda gwamnatin tarayya ta ambata a baya.

“Gwamnatin jihar, a ƙarƙashin jagorancin Dikko Umaru Radda ta bi sahun sauran jihohi wajen tabbatar da bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu ba tare da katsalada ba,” inji ɗanja wanda ya jaddada cewa ba iya bai wa ƙananan hukumomin ‘yancin tasarrufin kuɗinsu ne abin duba ba kaɗai, akwai buƙatar ba su damar yanke hukunci kan ayyukan da za su yi da kansu.

Shugaban ciyamomin, ya kuma yaba wa gwamnatin wajen ɓullo da sabbin hanyoyin ciyar da al’umma gaba yana mai bayyana hakan a matsayin ‘yar manuniya ta irin burin da Radda ke da shi na cicciɓa mutanen da ke can ƙasa-ƙasa.

“Wannan mataki zai ba wa al’umma damar shiga a dama da su kan al’amura da suka shafi rayuwarsu.”

“Shirin ya shafi bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu da kai tsaye domin gudanar da muhimman ayyuka kamar samar da ruwan sha da wutar lantarki da gina hanyoyi da sauran ayyuka na gina ɗan’Adam,” ya bayyana.

Ya kuma nuna kyakkyawan fatan da yake da shi a shekarar 2025 game da tattalin arziƙin jihar, musamman bunƙasa kuɗin shiga na ma’aunin GDP.

Ya buƙaci al’umma da su ba wa gwamnati haɗin kai wajen samun nasarar shirye-shiryen ciyar da rayuwarsu gaba da gwamnati ta ɓullo da su a matakai daban-daban.

“Akwai alamun samun bunƙasar tattalin arziƙi a cikin shekarar 2025 a ƙananan hukumomi,” in ji Danja. Ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya kan ɓullo da managartan tsare-tsare a jihar da ma ƙasa bakiɗaya.

“A ƙaramar hukumata,” inji ɗanja, “Akwai shirin ba da lamunin kuɗi da sauran tallafi daban-daban na gwamnatin tarayya domin rage wa al’umma raɗaɗin cire tallafin man fetur.”