Ƙananan hukumomin Bauchi sun fara cin gashin kansu, inji Gwamna Bala

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya shaidar cewa, ƙananan hukumomi ashirin na jiha a yanzu suna sarrafa kuɗaɗen su ne ba tare da wata katsalandan daga gwamnatin jiha ba, domin tun watan jiya na Nuwamba suka fara biyan albashin ma’aikatan su da kansu.

Gwamnan ya ce, “Tuni muka ƙarfafa zuciyar mallaka wa ƙananan hukukomin jiha, muna basu dukkan ɗaukacin kuɗaɗen su, kuma tuni suka fara biyan albashin ma’aikatan su da kansu.”

Sanata Bala Mohammed ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake karɓar tawagar Kiristocin jihar Bauchi a fadar gwamnati, lokacin bukukuwan Kiristanci na tunawa da Annabi Isah a satin da ya gabata da ƙungiyar CAN ta shirya, inda ya ce “mun yi farin cikin shaidar cewa, a watan Nuwamba da ya wuce, babu wani ma’aikacin ƙaramar hukuma da bai karɓi albashin sa ba.”

“Mun biya albashin ma’aikata, kuma muna cigaba da biyan albashi. Mutane da gangan suke kiran an ƙetare wasu wajen biyan albashi domin a haddasa rashin jituwa a tsakanin mu da su. 

“Babu mamaki cikin dubban ma’aikata da muke biyansu albashi, wasu ‘yan barandan da gangan su cizge albashin wasu ma’aikatan, amma dai abin fahimta shine, gwamnatin jiha tana bayar da wadatattun kuɗaɗe na biyan albashin dukkan ma’aikatan ta.”

Ya kuma bayyana cewar, gwamnatin tana matuƙar ƙoƙarin ta wajen ganin ba a samu wani giɓi ba kan biyan albashin ma’aikata, musamman yadda da gangan ake cire sunayen wasu ma’aikata daga cikin kundin biyan albashi, ya ƙara da cewar, Ofishin Shugaban Ma’aikata na jiha ya samar da na’urar jadawalin sunayen dukkan ma’aikata anan ma’aikatar kuɗi ta jiha.

Duk wanda ba a ba shi albashi ba, ya garzaya nan ma’aikatar kuɗi inda za a duba wannan jadawali, kuma da zarar an gane ba’a biya shi ba, nan take za a zurara masa kuɗaɗe cikin asusun sa na banki, kuma albashin koda na wata nawa ne bai samu ba.

“Dangane da biyan kuɗaɗen garatuti kuwa, mun gaji bashin ariyas na kuɗaɗen garatuti na kimanin naira biliyan ashirin da takwas daga gwamnatocin baya. Ba wani suddabaru da za mu iya yi.

“Za mu riƙa biyan garatuti ne kwatankwashin kuɗaɗen da suke shigowa raraitar gwamnati, bayan biyan albashi, kuma dangane da wannan tsari, kawo yanzu mun biya maqudan kuɗaɗe na garatuti, kuma duk lokacin da muka samu rarar kuɗaɗen’, abinda zamu riƙa yi kenan, domin muna da mushaƙar biyan haƙƙoƙin ma’aikata da suka yi ritaya,” inji gwamna.

Ya ƙara da cewar, gwamnati tana matuƙar ƙoƙarin inganta kundin biyan albashin ma’aikatan ta, bisa ingantaccen jadawalin biyan ma’aikata albashi, yana mai cewar, “wajibi ne mu samu daidai adadin ma’aikatan gwamnati.”

Gwamna Bala sai ya ce, “amma, a matsayin mu na Musulmai da Kiristoci, wajibi ne muji tsoron Allah, domin wasu ma’aikatan suna karvan albashi hannu bib-biyu a kowane wata, wasu kuma suna karɓan haramtattun alawus-alawaus.

“Kuna gani muna karɓan Naira miliyan bakwai daga asusun gwamnatin tarayya, amma mafi yawancin waɗannan kuɗaɗe sukan tafi ne wajen biyan albashin ma’aikata, amma duk da haka, sai kaji wasu na cewa basu samu albashi ba, tamkar almahara. Na sani a matsayina na ma’aikacin gwamnati, hakki ne a kaina na biya albashi, shi yasa nake biya, amma ba wai don an zaɓe ni saboda biyan albashi ba.”

Shugaban tawagar na Ƙungiyar CAN, wanda kuma shine shugaban ƙungiyar ta jiha, Reverend Abraham Yohanna ya bayyana godiyar sa wa gwamna saboda ci gaban da aka samu ƙarƙashin jagorancin sa cikin ƙanƙanin lokaci ƙasa da shekaru uku.

Rev. Abraham sai ya jinjina wa gwamna saboda abubuwa da yake yi wa al’ummar Kiristoci a jihar, yana mai bashi tabbacin cewar, za su rama wannan aniya ta gwamna, ya ƙara da cewar, tuni Kiristoci suka duƙufa yin addu’o’in samun nasarar gwamnatin Ƙauran Bauchi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *