Ƙanen tshohon Shugaban Ƙasa ‘Yar’adua ya lashe zaɓen sanatan Katsina ta Tsakiya

Daga UMAR GARBA a Katsina

Abdul’azizi Musa Yar’adua, ƙane ga tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua, ya samu nasarar lashe zaɓen ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Katsina ta tsakiya

Babban jami’in dake bayyana sakamako farfesa Aminu Ɗalhatu Kankia ne ya sanar da hakan inda ya bayyana cewar ‘Yar’adua ya samu ƙuri’a 153,512.

Inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Aminu Surajo Makera wanda ya samu ƙuri’a 152,140.

Sai kuma ɗan takarar jam’iyyar NNPP Gambo Abubakar Jally ke mara masu baya da ƙuri’a 1,605 sai kuma Muhammad Mustapha Kurfi na jam’iyyar SDP ya samu ƙuri’a 807 a yayin da Aminu Giɗe na jam’iyyar PRP ya samu ƙuri’a 781.

Sauran ‘yan takarar kujerar sanatan su ne Mannir Yusuf na ADC mai ƙuri’a 726 da kuma Muhammad Zainab Yusuf ta jam’iyyar NRM da ta samu ƙuri’a 583.