Daga AISHA ASAS
Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata, mun fara shimfiɗa kan yadda rashin ruwa ke zama silar samuwar curuta da dama, ciki kuwa har da tsakuwar ƙoda.
Mun kuma yi bayyani gamsashe da ka iya canza ra’ayin wadda ke yi wa ruwa kallon abin sha yayin da kawai aka ji ƙishirwa.
A wannan mako, za mu kawo wasu alamomi da za su iya ankarar da mu idan muna wasa da yi wa jikinmu ban ruwa.
1. Fitsari mai launi:
ɗaya daga cikin fitattun alamomin rashin ruwa a jikin ɗan adam akwai fitsari mai launin rawaya ko amber.
Domin a lokacin da jikinka ke da wadatattun ruwa, to fa fitsarin ka zai kasance fari ƙal, ko kuma yelo mai haske sosai (matuƙar dai babu wata cuta ta daban da ke haddasa hakan. Ko kuma wasu magunguna da muke sha da suke canza kalar fitsarinmu, kamar maganin TB)
Fitsari mai duhu yana nuna cewa jikinka na da ƙarancin ruwa da ka iya haifar da wata matsala kamar dai yadda muka faɗa a satin da ya gabata. Matakin gaggawa da ya kamata a ɗauka yayin da aka lura da hakan shi ne, linka adadin ruwan da ake sha a rana, har sai an lura da daidaituwar fitsarin.
2. Bushewar baki da maƙoshi:
Bushewar baki ko maƙoshi wata hanya ce ta magana da mai gangar jikin na cewa, yana tare da ƙarancin ruwa. Ta ya hakan ta ke kasancewa?
Idan jikin ɗan adam yana fama da ƙarancin ruwa, adadin yawun da zai samar zai ƙaranta, wanda hakan na nufin baki da maƙoshi zai shiga talaucin yawun da ke saka shi walwala, wanda zai haifar da bushewar shi.
Ba a iya bushewar matsalar za ta iya tsayawa ba, domin akwai yiwar ta haifar da warin baki, dalilin yawun baki na taka rawa a wanke baki, ta hanyar gusar da sauran abinci da ke maƙalewa a baki, ko ƙwayoyin cuta da ke shiga lokutan da muke buɗa baki, ko na ɓangaren abinda muke ci.
3. Bushewar fata:
Fata ɗaya ce daga cikin ɓangaren jiki mafi girma, kasancewar ita ke luluɓe da jiki bakiɗaya, don haka yayin da jiki ya rasa isashen ruwa, zai shiga layin ɓangarori da za su fi cutuwa, haka zai sa fatar ta shiga mawuyacin hali da ke kai wa ga bushewar ta. Samun isasshen ruwa a jiki zai taimaka a walwalar jiki, tare da tsare sa daga kamuwa da curutan fata da dama.
4.
Ciwon kai:
Rashin isassun ruwa a jiki na haifar da ciwon kai, dalilin rashin ruwa na tsayar