Ƙarairayin hukumomin leƙen asirin Amurka da Birtaniya ba za su tsorata kowa ba

Daga CMG HAUSA

Ƙasashen Sin da Jamus, sun daddale wata babbar kwangila da darajar ta ta kai kuɗin Euro miliyan 200, ta ayyukan hadin gwiwar kansuwanci guda goma a ranar 7 ga watan nan, lamarin da ya nuna cewa, ƙasar Sin tana kara jawo hankalin masu zuba jari na ƙetare, kuma hakan tamkar martani ne ga ƙarairayin da hukumomin leƙen asirin ƙasashen Amurka da Birtaniya suke maimaitawa, domin tsorata kamfanonin ƙasashen yamma.

Shugaban hukumar FBI ta Amurka Christopher Wray, da shugaban hukumar MI5 ta Birtaniya Ken McCallum, sun yi kashedin haɗin gwiwa, yayin taron watsa labaran da aka shirya a birnin Landan, fadar mulkin Birtaniya a ranar 6 ga watan nan, cewa masu leƙen asiri, da masu satar bayanai ta yanar gizo na ƙasar Sin, suna satar ‘yancin mallakar fasaha na ƙasashen yamma, domin cimma burin ƙasar na jagorancin fasahohin muhimman sana’o’in zamani.

Ƙarairayin hukumomin sun nuna aimihin halinsu, na “baza ƙarya da yaudara da sata”, Domin ko kaɗan, ba su taba gabatar da shaidun dake tabbatar da zargin ba, amma haƙiƙanin matakan leken asirin tattalin arziki, da satar bayanai ta yanar gizo da suka aiwatar kan ƙasar Sin suna da dama.

Haƙiƙanin abubuwa sun shaida cewa, ƙarairayin waɗanda aka baza game da ƙasar Sin, da yunƙurin raba kawuna, su ne ainihin barazanar da za ta haifar da illa ga Amurka da ƙasashen yamma.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa