Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta kashe Naira miliyan 85 wajen gyara da faɗaɗa sakatariyar Ƙaramar hukumar.
Shugaban ƙaramar hukumar, Malam Anas Isa, ya sanar da haka lokacin da yake hira da manema labarai a ofishin sa a Ƙanƙara.
Ya bayyana cewa an gudanar da gyare-gyaren a ɗakin taro, ofisoshin shugabannin sassa sassa da sabunta katangar ƙaramar hukumar.
Malam Anas ya ce tunda aka gina sakatariyar ƙaramar hukumar ba a taɓa yi mata ko da kwaskwarima ba balle a sami damar faɗaɗa ginin.
Da an kammala aikin gyaran sakatariyar za ta kasance wanda tafi kowace ta fannin tsarin ginin da samar da kayan aiki na zamani wa ma’aikatan.
Rashin tsaro a shekarar baya yasa ma’aikatan ƙaramar hukumar ƙauracewa sakatariyar, “wannan ma ya sa sakatariyar ta kai gab da rugujewa,” inji Anas.
Akan harkar tsaro kuwa a ƙaramar hukumar, Malam Anas ya bayyana yankin a matsayin yankin da yafi Kowane bala’in hare haren ‘yan bindiga.
“Amma ƙoƙarin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ya yi na samar da jami’an tsaro na al’umma CWC ya taimaka gaya wajen ciwo ƙarfin ta’adanci a yankin”cewar shugaban ƙaramar hukumar.
Ya bayyana farin cikin sa yadda al’amura na yau da kullum suka dawo a yankin.
Matsalar da ake fama da shi a yakin yanzu, mafi yawan masu kawo hare hare baƙi ne da suka fito daga Jihar Kaduna inda aka yi sasantawa a tsakanin ‘yan ta’addan da gwamnatin Jihar Kaduna.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana wasu aikace-aikace da gwamnatin sa da ta Dikko Raɗɗa suka aiwatar da suka haɗa da samar da ruwan sha da hanyoyi, ilimi da kiyon lafiya a mayan garuruwan Wawar kaza, ƙetare da garin Ƙanƙara.