Ƙaramar hukumar Ɓaɓura ta shirya tsaf domin fuskantar musabaƙar Alƙur’ani

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse

Bayanai sun nuna ƙaramar hukumar Ɓaɓura ta shirya Tsaf domin tinkarar gasar karatun musabaƙar alƙur’ani da gwamnatin Jihar Jigawa ta ke Shirin gudanarwa.

A ƙoƙarin ta na ƙara haɓaka harkar ilimin addinin Musulunci, ƙaramar hukumar Ɓaɓura da ke Jihar Jigawa ta gudanar da taron mubasaƙar karatun alƙur’ani mai tsarki karo na 38.

A jawabin sa wajen buɗe karatun musabaƙar, shugaban ƙaramar hukumar ta Ɓaɓura Malam Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewar Ƙaramar hukumar tana da tsare-tsare na bunƙasa ilimi musamman a matakin farko. A don haka, ya buƙaci al’ummar yankin musamman masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi da su haɗa hannu domin ɗaga darajar ilimi a yankin.

Malam Hamisu Garu, yana mai kira ga ɗaliban da za su yi karatu su yi hazaƙa don ƙaramar hukumar ta sami kakkyawan wakilci a gasa ta jihar.

Shima a nasa jawabin, sakataren ilimi na yankin Malam Zubairu Dabo, ya bayyana godiyar su bisa ɗaukar nauyin masabaƙar da ƙaramar hukumar tayi da kuma godiya kan sauran tallafi da ake yiwa ma’aikatar.

Wakilin Radio Nigeria ya aiko mana da rahoton cewar, Malam Ayuba Sabo shine alƙalin da ya jagoranci masabaƙar karatun Al’Qurani mai girma a ƙaramar hukumar ta Ɓaɓura.