Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙaramar Hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Hon. Emmanuel Leweh ya rasu.
Majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa Leweh ya rasu ne a wani asibitin Abuja bayan fama da ya yi rashin lafiya.
Marigayin ya kwanta a asibiti ne tun bayan da ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar a ‘yan kwanakin da suka gabata inda aka kwashe zuwa asibiti don ba shi kulawar da ta dace amma a ƙarshe rai ya yi halinsa.
Kimanin watanni uku kenan da aka rantsar da Leweh a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Akwanga.
Cikakken rahoto na nan tafe….