Ƙaramar Hukumar Bichi ta cilla yawan ƙuri’un Gawuna sama

Daga WAKILINMU

Ƙuri’ar yankin Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, ta taimaka wajen cilla yawan ƙuri’un ɗan takarar Gwamna na APC sama wanda hakan ya sake bai wa ɗan takarar damar shige gaban takwararansa na jam’iyyar NNPP.

Da fari Abba Kabiru Yusuf ne ya kasance kan gaba a yawan ƙuri’u, kafin daga bisani lamarin ya juya kan Nasir Gawuna na APC.

Bayan wani lokaci NNPP ta sake shigewa gaba har zuwa lokacin da aka bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Bichi, a cibiyar tattara sakamakon zaɓen.

Daga nan ne Nasir Gawuna na APC ya sake tsere wa Abba a yawan ƙuri’u inda ya tashi da ƙuri’u 444,537 sannan abokin hamayyarsa na NNPP na da 427,496.

Wanda hakan ya samar da bambancin ƙuri’a 17,041a tsakanin manyan ‘yan takarar.