Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Sakataran Ilimi na ƙaramar Hukumar Birnin Kano kuma mataimakin shugaban ƙungiyar Malamai NUT, ya bayyana cewa ƙaramar hukumar birnin Kano na daga cikin sahun gaba a ƙananan hukumomi 44 na Kano da suka amfana da tallafin dubunnan kayan makaranta na sawa ga ‘yan firamare a ƙaramar hukumar baki ɗaya, musamman wanda suka shiga aji ɗaya a wannan ƙaramar hukumar birnin Kano da kewaye, kamar dai yadda sakataren ilimin ya bayyana wa manema labarai a makon da ya gabata.
Kwamared Nura ya bayyana cewa, “zuwan gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu cigaba ta kowane fanni musamman ganin yadda a kasafin kuɗin 2003 aka ware kashi 30 cikin 100 kan ilimi 2004 kashi 31 cikin 100 to ba shakka kwalliya tana biyan kuɗin sabulu musamman mu malaman makaranta ta hanyar wadata mu da kayan aiki da gyaran da CRC ta ke yi a ko ina a jihar nan wanda a baya mu malaman makaranta sai dai mu saya alli don mu koyar da ɗalibai da kuɗinmu, ga kuma biyan albashi cikakke duk wata ba a yanke albashi da dai sauransu.”
A ƙarshe sakataren ilimi ES Malam Nura Sulaiman ya bayyana cewa abin da yake ƙara faranta musu rai shi ne yadda aka samu wadatar malamai a wannan ƙaramar hukuma da ma Kano baki ɗaya ga kuma ƙarin girma na shekara-shekara babu ɓata lokacin wanda a baya abubuwa sun rikirkice amma yanzu zuwan gwamna Kano Abba sai dai godiya kuma muna yabawa shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na Kano da maaikatar ilimi da sauran masu ruwa da tsaki irin ƙungiyar iyaye da malaman makaranta, sarakuna ,Hakimai, Dagatai masu unguwani ƙarkashin fadar masarautar Kano bisa jagoranci Malam Muhammad Sunusi na II.