Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta sa ƙafar wando da masu sare itace

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa ta yi fice wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa sa kawo ci gaba mai ma’ana.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Birnin Kudu, Alhaji Magaji Yusuf Gigo ya tabbatar da hakan ga manema labarai a lokacin da ya gana da su a ofishinsa da ke Birnin Kudu.

Ya ci gaba da cewar ƙaramar hukumar ta yi ƙoƙari wajen gyaran asibitoci tare da inganta waɗanda take da su da nufin bunƙasa harkokin kiwon lafiya.

Haka zalika, ƙaramar hukumar ta samar da ruwan sha mai tsafta domin amfanin al’ummarsu.

Ya kuma koka game da ƙarancin ruwan sha da ƙaramar hukumar take fuskanta saboda yawan al’umma, ya ce akwai buƙatar gwamnatin jihar Jgawa da ma gwamnatin tarayya su shigo cikin harkar samar da wadataccen ruwan sha a yankin, domin amfanin mazauna yankin.

Ya ce aikin samar da ruwan sha a yankin al’amari ne da ya fi ƙarfin ƙaramar hukumar ita kaɗai, ya zama dole gwamnatocin biyu su shigo cikin tafiyar su agaza domin ceto mazauna yankin daga cikin halin da suka samu kansu a ciki.

Ya ci gaba da cewar ƙaramar hukumar ta yi iyakacin baƙin ƙoƙarinta wajen magance matsalar batirin injinan samar da ruwan sha, ya ce dama shine yake saurin mutuwa kuma yanzu haka sun sayi batira biyar da ake amfani da su.

Da ya juya wajen kiwon lafiya ya ce ƙaramar hukumar ta gina asibitoci ta kuma inganta waɗanda take da su tare da samar da magunguna musamman a lokacin yaɗuwar cutar Kwalara da ta faru kwanan baya.

Ya ce dukkan masu madafun iko da suke cikin gwamnati a yankin tun daga kan sanata, ‘yan majalisar tarayya da na jiha sun bada gudunmawarsu domin yaƙar cutar Kwalara a wancan lokacin da annobar ta faru.

A ɓangaren ilimi kuma ƙaramar hukumar ta buga littatafan karatu na ‘yan firamare kwafi dubu goma mai ɗauke da hoton gwamna aka raba kyauta a makarantun yankin da nufin ƙara wa ɗalibai ƙarfin gwiwa akan karatu.

Alhaji Magaji Yusuf ya ƙara da cewar ƙaramar hukumar ta gina babbar maƙabartar garin da bulon siminti. Ƙaramar hukumar ta kashe Naira miliyan shida, kuma ta gina rijiyar tuƙa-tuƙa a cikin maƙabartar domin amfanin al’umma.

A ɓangaren samar da ruwan sha ƙaramar hukumar ta sayi kayan aikin ruwan sha na Naira miliyan biyar da nufin wadata al’ummar yankin da ruwan sha mai tsafta.

Magaji Yusuf ya ƙara da cewar ƙaramar hukumar ta saya wa shugaban ƙaramar hukumar motar hawa kuma ta gyara motoci biyar na ƙaramar hukumar domin amfanin manyan ma’aikatan ƙaramar hukumar.

Ya ƙara da cewar yana cikin burinsu na samar da hanyoyin mota a lunguna da saqo wajen da babu hanyoyin mota. Ƙauyukan da hanyoyin za su shafa sun haɗa da Surko da Giwa da kuma wasu manyan garuruwa da hanyoyin motar bai shafesu ba.

Ya ci gaba da cewar qaramar hukumar ta gina tuƙa-tuƙa bakwai a yankunan karkara kowanne ɗaya a kan Naira 450,000.

Ya ci gaba da cewar ƙaramar hukumar za ta mayar da hankali ne wajen ayyukan raya ƙasa a shekara mai zuwa da suka haɗa da samar da ruwan sha ga al’ummar ƙaramar hukumar Birnin Kudu musamman cikin gari da ƙauyuka, kuma ƙaramar hukumar za ta sa ido akan masu sare itatuwa barkatai.

Ya ce ƙaramar hukumar ba za ta sanya ido wasu marasa kishin al’umma suna kashe bishiyoyin suna qone su suna yin gawayi da su haka kawai ba.

Haka zalika shugaban qaramar hukumar ya ce nan gaba kaɗan ƙaramar hukumar za ta yi wata doka da za ta hana ‘yan acaɓa ɗaukar mata fiye da ɗaya a kan babur.

Ya ce ƙaramar hukumar za ta haɗa kai da jami’an tsaro na ‘yan sanda da ‘yan sintiri da ‘yan Hisba wajen kama duk wanda ya karya dokar. Kuma za a sanya tara mai tsanani akan duk wanda ya karya dokar, domin ya zama darasi akan duk wanda ya yi wa dokar kunnen uwar shegu domin hakan ya zama darasi akan waɗanda suke son karya dokar.

Ta fuskar wasan motsa jiki kuwa matasan Brnin Kudu sune suka cinye a matsayin matasan da suka fi kowa ɗa’a a wata gasar fidda zakaru da aka yi a jihar Gombe a kwanan baya.