Ƙaramar Hukumar Dala na bada abincin buɗe baki kyauta ga al’ummar yankin – Sanda Gabasawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

A cigaba da ɗaukar nauyin ciyarwa da Gwamnatin Jihar Kano take a ƙananan hukumomi dake ƙwaryar birnin Kano, Ƙaramar Hukumar Dala na raba abincin buɗe baki kyauta da ake dafawa a cibiyoyi 19 dake yankin.

Shugaban sashen kula da jin daɗi da walwalar jama’a na  yankin ƙaramar hukumar, Alhaji Ibrahim Sanda Gabasawa shine ya bayyana hakan ga ‘yan jarida.

Ya ce yanzu haka kullum Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje tana ɗaukar nauyin dafa abinci da ake ciyarwa kyauta a cibiyoyi guda 15 na ƙaramar hukumar ta Dala.

Domin tallafa wa wannan aikin alheri da gwamnatin jihar take don ƙara faɗaɗa lamarin Ƙaramar Hukumar Dala bisa jagorancin Hon. Ibrahim Suleiman Ɗan’isle ta ƙara cibiyoyi  huɗu akai wanda yanzu haka ana ciyarwar ne zuwa cibiyoyi 19 a yankuna daban-daban na yankin.

Shugaban sashen kula da jin daɗi da walwalar na Dala ya ce a kowace cibiya ana ciyar da mutane 300 da abinci kala-kala da suka haɗa da shinkafa, alale, kunu da sauran launukan abinci iri da dama.

Alhaji Ibrahim Sanda Gabasawa ya ce ƙaramar hukumar tana mutuƙar sa ido da lura don tabbatar da an samar da abinci mai tsafta da inganci ta tabbatar da tsaftar wajen girkin da ingancin abinda ake girkawa tare da tabbatar da ɗanɗano mai gamsarwa.

Shugaban sashen walwala da jin daɗin jama’ar na Dala ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa cigaba da tabbatar da tsarin na ciyarwar da aka jima ana yi da yake taimakawa wajen ragewa ɗimbin mutane raɗaɗi. Sannan ya yi kira ga gwamnati ta ƙara faɗaɗa ciyarwar don game dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *