Ƙaramar Sallah: Sarkin Musulmi ya buƙaci a nemi jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis

Majalisar Ƙoli Kan Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA) ta yi kira ga al’ummar Musulmin ƙasar nan da su nemi jinjirin watan Shawwal na shekarar 1444 A.H ranar Alhamis, 29 ga Ramadan 1444 A.H daidai da 20 ga Afrilu, 2023.

NSCIA ta buƙaci Musulmi su nemi watan da zarar rana ta faɗi a wannan rana.

Wannan kira na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce Shugaban NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ne ya yi wannan kira bisa shawarar Kwamitin Duban Wata na Ƙasa (NMSC).

Sanarwar ta ƙara da cewa, idan Allah Ya sa aka wata tare da cika sharuɗɗan da suka dace, Sarkin Musuli Abubakar zai bayyana Juma’a, 21 ga Afrilun 2023 a matsayin 1 ga watan Shawwal wadda kuma za ta kasance ranar Ƙaramar Sallah (Eid-El-Fitr).

Haka nan, ta ce idan kuwa ba a ga watan ba, kenan ranar Asabar, 22 ga Afrilun 2023, za ta kasance ranar Ƙaramar Sallah.

Majalisar ta yi fatan kammala azumin Ramadan cikin nasara ga al’ummar Musulmi, kana ta buƙaci jama’a a bi hanyoyin da suka dace wajen isar da saƙo idan Allah Ya sa aka ga wata a yankunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *