Ƙaramin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin Sin da Nijeriya ya gudanar da taronsa na farko

Daga CMG HAUSA

A ranar 10 ga watan Maris, ƙaramin kwamitin siyasa da diflomasiyya na babban kwamitin tsakanin ƙasashen Sin da Najeriya ya gudanar da taronsa na farko ta kafar bidiyo, wanda Deng Li, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin, da Zubairu Dada, karamin ministan harkokin wajen Najeriya suka jagoranta.

Ɓangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu game da hulɗar dake tsakanin ƙasashen biyu, da kuma haɗin gwiwarsu a fannoni daban-daban, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan batun aiwatar da sakamakon da aka samu a taron ministoci karo na 8 na taron dandalin tattaunawar haɗin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, kana sun zurfafa musayar ra’ayi game da batun ƙarfafa hulɗar siyasa, da taimaka wa juna tsakanin ɓangarori daban-daban, da kuma faɗaɗa haɗin gwiwarsu a ƙananan ofisoshin jakadanci na ƙasashen biyu.

Ɓangarorin biyu za su aiwatar da ra’ayi ɗaya da shugaba Xi Jinping, da shugaba Muhammadu Buhari suka cimma, game da bunƙasa hulɗar ƙasashen biyu, da ingiza matakan aiwatar da sakamakon da aka samu a taron FOCAC, da ci gaba da zurfafa haƙiƙanin haɗin gwiwarsu a dukkan fannoni, da kuma daga matsayin muhimmiyar hulɗar dake tsakaninsu zuwa matsayin koli.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *