Ƙaramin sani ƙuƙumi

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Bahaushe ya na cewa, “ƙaramin sani ƙuƙumi” kuma idan ka kalli wannan magana tsaf, za ka gane cewa har gara jahilci da ita, domin jahilci ba zai ba ka damar kutse a ilimi ko wani abu sananne ba, amma shi mai ƙaramin sani daidai ya ke da zancen Larabawa na hikima da ke cewa “wanda bai sani ba, amma bai san bai san bai sani ba, wawa ne, ku ƙaurace masa”.

Da yawa cikin matasanmu ’yan boko da kansu ke hayaƙi saboda ɗan guntun ilimi da su ke zaton su na da shi, ya kan jefa su cikin wannan aji na ƙaramin sani. Irin waɗannan matasa na da yawa a wannan saha ta Facebook. Akwai waɗanda za ka ga masana na yammacin Turai na matuƙar burge su, saboda iya bayani da dogon Turanci ko kimiyya. Don haka yadda su ke imani da su ba sa yin imani da addininsu ko masanan Musulunci.

Akwai wani fitaccen mulhidi, Dan luwaɗi, Bayahude, wanda a yanzu haka yake auren namiji ɗan uwansa, wanda ake kira da Yuɓal Noah Hariri, maganarsa a wajen irin waɗannan masu ƙaramin sani, ta fi ta Allah da manzonsa karɓuwa a wajensu.

Haƙiƙa babu tantama, ƙalilan mutane masana ilimi a wannan duniyar tamu za su yi kafaɗa-da-kafaɗa da wannan Bayahude wajen sanin kimiyya da kuma iya bayani. Komai iliminka idan ka saurare shi, ko ka karanta rubuce-rubucensa sai ka ƙaru da wani ilimi. Amma illar ita ce, matuƙar ka na cikin ajin ƙaramin sani, haƙiƙa ka na cikin haɗarin karɓar da’awarsa ba tare da ka san illar inda ya jefa ka ba.

Akwai shahararren littafinsa “Homo Deus” wanda ya ke matuƙar burge ’yan ƙaramin sani sosai, amma hatta daga taken littafin ka san cewa akwai wata a kullalliya a ƙasa. “Homo” na nufin “Mutum” ita kuma “Deus” na nufin ” Allah”, wato ma’ana “Mutum Allah ne”. Maƙasudin yin wannan littafin shine domin yaɗa aƙidar Mulhidanci, wato cewa babu Allah, ta hanyar amfani da kimiyya wajen nuna cewa duk wani abu kimiyya na iya warware shi.

Wannan tsabagen ƙ arya ce kuma babu mai yadda da ita sai ’yan ajin ƙaramin sani ko jahilai. Na farko dai abubuwa da suka shafi rayuwar ɗan’adam mafi mahimmanci guda biyar, duk sun gagari samuwar cikakken bayani daga kimiyya. Na farko asalin halitta (Origin of Uniɓerse) daga ina ta faro? Sannan ina aka sami rai (Origin of life)? Mene ne hankali (consciousness)? Mece ce mutuwa, za a iya yaƙar ta (Death) da kuma iya hasashen me zai iya faruwa nan da daƙiƙa mai zuwa (Predict future). Waɗannan abubuwa ne da su ka shafi rayuwar mu na ƙut-da-ƙut, amma duk sun gagari kimiyya.

Idan mu ka koma kan littafin Hariri na Homo Deus, a ciki ya yaɗa aƙidoji guda huɗu, waɗanda kowannensu a karan-kansa shi kaɗai, idan ka yi imani da shi, to haƙiƙa ya rushe dukkan addinai:

1. Ya nuna babu wani abu rai (soul)

2. Idan an mutu babu tashi

3. Za a iya daina mutuwa

4. Dan adam shine Allah, ba wani Allah

Duk wanda ya yi imani da waɗannan abubuwa ya tashi daga Musulmi, domin duk wata koyarwa ta Musulunci ya rushe ta. Amma duk wanda da ma ya zaɓi zama ‘Atheist’ babu laifin idan ya yi Imani da hakan.

Gargaɗina ga masu ƙaramin ilimi shine, kada a yaudare su da sunan kimiyya a jefa su cikin aƙidar ‘atheism’, domin hanyar da ‘atheist’ suka ɗauka ta wa’azi shine amfani da kimiyyar ƙarya ga waɗanda ba su da ilimi, kuma hakan na tasiri ga matasa sosai. Shi ya sa na kira shi a wata maƙala ta da na yi da Turanci da “Most dangerous author”, saboda ya na da ilimi da iya bayani fiye da akasarin masana na wannan zamani.

Ban ce a daina karanta shi ba, domin sai ka san sharri za ka iya guje masa. Amma dai a karanta shi “with a grain of salt”, a ɗauki abinda za a ƙaru, a jefa masa Mulhidancinsa.

Sannan matasa ku lura, duk wanda ku ka ga yana zaƙalƙalewa a kan kimiyya ita ce komai kuma duk abinda ta ce shine daidai, ko ya na fifita kimiyya a kan addini, sannan ya na nuna cewa babu wata alaka tsakanin kimiyya da addini, to wallahi cikin biyu: ko dai ya kasance a ajin ƙaramin sani domin ya na da jahilcin kimiyya da kuma addinin, ko kuma Mulhidi ne mai yin Taƙiyya wajen yaɗa aƙidar ta Mulhidanci.

Ali manazarci ne mazaunin Kano