Ƙaranci da tsananin tsadar burodi a Nijeriya

’Yan Nijeriya na fama da ƙaranci da kuma tsananin tsadar burodi bayan masu gidajen burodi sun fara yajin aiki a faɗin ƙasar.

A safiyar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne Babbar Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi ta fara yajin aiki, saboda abin da ta kira tashin gwauron zabon kayan haɗa burodi.

Tun kafin fara yajin aikin nasu da zai ɗauki tsawon kwana huɗu, ’yan Nijeriya ke ta bayyana damuwa, bayan a wasu wuraren an ninka farashinsa.

Shugaban Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi da Dangoginsu ta Ƙasa, Emmanuel Onuorah tare da Kakakin ƙungiyar, Babalola Thomas sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 cikin 100 da take karɓa na bunƙasa noman alkama daga hannunsu.

Sun kuma buqaci Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta rage yawan kuɗin da mambobin ƙungiyar ke biya na Naira 154,000 kan jinkirin sabunta lasisi.

Sun kuma bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya riƙa ba wa masu kamfanonin burodi rancen da aka ware wa matsakaita da ƙananan masana’antu.

Haka kuma suna kira da a’a dakatar da yawan hukumomin da ke sanya ido kan harkokin sana’ar burodi.

Muna kira ga gwamnati a dukkan matakai, da ta duba halin da mutanen ƙasar nan ke ciki, ta kuma sani cewa mutane da dama na karen kumallo ne da burodi.

Daga Nafisah Auwal, 08141306201.