Ƙarancin kuɗi: Buhari bai hana Malami da Emefiele bin umarnin kotu ba, cewar Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu inda Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗa wa Babban Lauyan Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele cewa su bijire wa umarnin Kotun Ƙoli game da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N1000, N500 da N200 zuwa Disamban bana ba.

Babban kakakin Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja.

Ya ce Shugaba Buhari bai umarci Malami da Emefiele su ƙi yin biyayya ga umarnin na kotu ba.

Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar ta ce: “Fadar Shugaban Ƙasa na raddi kan wasu batutuwa da suka shafi ƙasa cewa Shugaba Buhari bai ce komai ba game da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke dangane tsoffin N500 da N1,000.

“A gaskiya babu inda Shugaban Ƙasa ya faɗa wa Babban Lauyan Ƙasa da Gwamnan CBN cewa su bijire wa kowanne umarnin da kotu ta bayar.

“Tun bayan da aka rantsar da Shugaban Ƙasa a 2015, bai taɓa ce ma wani ya bijire wa umarnin kotu ba. Musamman kuma ganin cewa babu yadda za a bi tsari na dimokraɗiyya ba tare da bin doka ba,” in ji sanarwar.

Garba Shehu ya ce duk da irin wahalar da ke tattare da sabbin dokokin da CBN ya fitar, hakan bai hana ‘yan ƙasa yin na’am da hakan ba saboda sanin cewa dokokin za su taka rawa wajen yaƙi da rashawa da ta’addanci da sauransu a ƙasa.

Don haka ya ce a daina ganin laifin Shugaban Ƙasa dangane da ƙaranci Naira da ake fuskanta duk da umarnin kotu, yana mai cewa Buhari bai hana CBN cika umarnin kotu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *