Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban A”umma, wato CITAD, da haɗin gwiwar ƙungiyar ƙwararru ta Jihar Kano sun shirya taron yini ɗaya da ya yi duba akan matsalar wutar lantarki da yadda ya shafi tattalin arziki na al’ummar Arewacin Nijeriya domin samar da mafita.
Taron da ya gudana a cibiyar ta CITAD da ke Kano a ranar Litinin, ya yi duba akan sha’anin samar da lantarki da inganta zamantakewar al’ummar Arewa.
Matsalar rashin wutar lantarki a Arewa da ta samo asali daga lalacewar turakun lantarki zuwa arewacin Nijeriya daga Kudanci, haɗakar waɗannan ƙungiyoyi biyu sun nusar kuma sun faɗakar kan muhimmancin yin magana da murya ɗaya.
Malam Ahmad Sajo wanda tsohon kwamishinan yaɗa labarai a jihar Adamawa ne bayyana cewa dole ne a yi abin da ya dace a dawo da wutar arewacin na Nijeriya domin saboda asarar da rashin wutar ya haifar a fannin lafiya da kasuwanci da hanyoyi da yawa, ba bu abinda za mu fahimta in dai ba a dawo da wutar ba, ya kuma zama dole a inganta tsaro a Arewa.
Ya ƙara da cewa, “Ba mu da injinan da suke ba da wutar a Arewa in banda a Arewa ta Tsakiya, babu a Arewa ta Yamma, babu a Arewa ta Gabas, hakan ba alheri ba ne ga Arewa.
“A lokacin Obasanjo aka mayar da wurin da ake rarraba lantarkin Nijeriya zuwa Osogbo, sai aka yi mana layuka biyu zuwa Arewa, wasu na da layuka biyar, bakwai, takwas har tara. Dole sai an yi sabbi zuwa a Arewa, mu kafa kamfanoni ko injina masu samar da lantarki a jihohinmu na aArewa.
“Babban abin da ya kamata mu yi mu fara tunani kan wasu hanyoyi na samun lantarki, ana amfani da hasken rana da gudun iska a samu lantarki.”
A cewar tsohon kwamishina Sajo, babban ƙalubalen da ke gaban al’ummar Arewa shi ne su san irin shugabannin da suke turawa Abuja don wakiltarsu.
Engr. Kassim Abdullahi Burkullu shi ne shugaban sashin rarraba wutar lantaki a kamfanin KEDCO mai kula jihohin Kano da Jigawa da Katsina, ya bayyana dalilin da suka jawo rashin wutar da ake fama da ita a Arewacin na Nijeriya inda ya ce:
“Layin lantarki na farko da ya fara samun matsala shi ne na Shiroro zuwa Kaduna ranar 9 ga Satumba, sai muka koma layi na biyu, a ranar 13 ga Oktoba wannan ne wasu marasa kishin ƙasa suka lalata biyu daga cikin turakunsa, dalilin haka ne kamfanin da ke samar da lantarkin TCN ya mayar da layin wutar da ke zuwa Kano da sauran wurare ta hanyar Makurdi zuwa Jos shi ne ranar Litinin da ta gabata aka samu matsala a kan wannan layi.
“Amma yanzu haka injiniyoyi suna aiki a kan layin, har sun jarraba layin ma, amma idan sun gama sai a sake samun wata matsalar. Saboda wata matsalar da ba su sani ba, amma suna aiki a kullum in sun kammala aikin wuta za ta dawo,” inji Burkullu.
Daga cikin ƙuduroin da taron ya aminta da su sun haɗar da buƙatar ganin masu zuba jari sun shigo harkar lantarki sosai, da gyara layukan lantarki na ƙasa da buƙatar haɗa kai da shugabanci nagari da kuma buƙatar samar manufa ta yanki da sauransu.
Taron dai ya samu halartar masana da ƙwararru a faɗin ƙasar, inda wasu suka yi amfani da Manhajar Zoom wajen bada gudunmarsu don ganin an samar wa da Arewa mafita.