Ƙarancin mai ya kunno kai sa’o’i bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin mai

Da alama layukan ababen hawa a gidajen mai ya dawo a Jihar Legas sa’o’i bayan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai.

Bayanai sun ce an ga cinkoson ababen hawa a gidajen mai ɗin NNPC a yankunan Ikeja da Alausa waɗanda ke jiran su sha mai.

Ya zuwa haɗa wannan labari, an ga da daman gidan mai masu zaman kansu a yankunan ba su sayar da mai.

A jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce masu ƙumbar susa kaɗai ke amfna da tallafin mai amma ban da talakawa.

Ya ce, “Mun yaba da ƙoƙarin gwamnati mai barin gado bisa ƙoƙarin da ta yi game da tallafin mai wanda galibi ya fi amfanar shafaffu da mai.”

Ya ƙara da cewa, maimakon ci gaba da narka kuɗi wajen tallafin mai wanda ba ya amfanar talakan ƙasa, “Gara mu karkatar da kuɗin zuwa hanyoyin da ‘yan ƙasa za su amfana, wajen samar da ababen more rayuwa, inganta fannin lafiya da ilimi da samar da ayyukan da za su ingata rayuwar miliyoyin jama’a.”

Ya ƙara da cewa, zai dubi koke-koken ‘yan ƙasa kan batun haraji domin bunƙasa tattalin arziki da kwaɗaita wa ‘yan kasuwa su shigo su zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *