Ƙarancin ruwa na jikkata majinyata a asibitin Dutse

*Gwamnatin Jigawa ta samar da inji – Shugaban asibitin

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙarancin ruwan sha ya addabi babban asibitin kwanciya na Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, wato Dutse General Hospital, lamarin da ya sa marasa lafiya da masu zaman jiyya yin gararambar neman ruwan sha a unguwannin Maranjuwa, Fagoji Bakwato da bakin kasuwar ’yan Tifa da ke birnin na Dutse.

Kamar yadda binciken Wakilin Blueprint Manhaja ya nuna, ta kai ta kawo marasa lafiya da masu zaman jiyya sun koma yin alwala da ruwan leda da ake kira da ‘pure water’ na Naira 20 ƙwaya ɗaya da suke saya a wajen masu tallan ruwa, saboda ƙarancin ruwan sha da asibitin ya ke fuskanta.

Asibitin ya fara fuskantar wannan matsala ta rashin ruwa ne kimanin tsawon makonni, al’amari lamarin da ya sa aka samu ƙazanta a mafiya yawan banɗakunan da ke harabar asibitin, musamman waɗanda marasa lafiya su ke amfani da su. Hakan ya sa marasa lafiya da masu zaman jiyya yin fitsari da bahaya a wasu sassa na cikin asibitin.

Wannan matsala ta ƙarancin ruwa hatta fulawowin da aka dasa a wasu sassa na asibitin ya sa sun shiga mawuyacin hali yayin da fanfuna suka ƙafe ƙaraf tamkar a sahara, babu ko da ɗigon ruwa.

A yayin da ya ke tabbatar da labarin, Shugaban Asibitin, Dr Abubakar Omonomo, ya ce, labarin matsalar ƙarancin ruwan shan a asibitin gaskiya ne, inda ƙara da cewa, matsalar ta faru ne sakamakon matsalar rashin samun wutar lantarki, saboda kasancewar asibitin ba ya samun wutar lantarki, kamar yadda ya kamata. Ya kuma yi ƙorafin cewar, rijiyarsu ta rufta. Don haka ta na buƙatar yashewa, inda yanzu haka a na ƙoƙarin yashe ta, domin ganin ruwan sha a asibitin ya wadata.

Sai dai ya ƙara da cewa, yanzu Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar ma su da injin janareto da za su yi amfani da shi wajen samar da ruwan sha a asibitin.

Ya kuma ce, akwai buƙatar gwamnati ta samar da qarin rijiyoyi a cikin asibitin, domin ganin an samar da wadataccen ruwan sha a asibitin da nufin kauce wa irin wannan matsala nan gaba.

Ya kuma roki marasa lafiya da Mmasu zaman jinya da ke asibitin su yi haƙuri dangane da al’amarin da ya faru, ya ce, ƙarancin ruwan ya faru ne, saboda matsalar ƙarancin wutar.

Ya ce, yanzu hukumomin asibitin da hukumar bayar da ruwan sha ta asibitin sun duƙufa wajen shawo kan matsalar, don ganin an samar da ruwan sha a asibitin, domin amfaninsu.