Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu mazauna birnin Kalaba sun nuna fargaba kan rashin samun kuɗaɗe daga bankuna da kuma na’urar ATM a cikin birnin.
Mazauna yankin da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Kalaba a ranar Laraba, sun ce samun kuɗi ya yi matuƙar wahala a cikin mako guda da ya wuce.
NAN ta ruwaito cewa an samu dogayen layukan ATM a kewayen birnin yayin da mazauna garin ke kokawa wajen samun kuɗi.
NAN ta kuma ƙara da cewa lamarin na yin ta’adi a kan ƙananan ‘yan kasuwa da ba su da na’urar POS da kuma wuraren hada-hadar banki ta yanar gizo.
A halin yanzu, masu gudanar da POS suna cin gajiyar halin da ake ciki don neman ƙarin cajin ma’amala.
Abel Uwem, wani malami mazaunin Kalaba, ya bayyana lamarin a matsayin ‘mummuna da azaba, kuma ya buƙaci bankunan da su samar da tsabar kuɗi ga kwastomominsu.
“Yaya za mu iya jurewa lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara ba tare da tsabar kuɗi ba? Yawancin injinan ATM na garin ba sa ba da kuɗi,” inji shi.
Anekan Bassey, wani makanike ya bayyana cewa matsalar ta biyo bayan ƙin baiwa kwastomominsu kuɗi sama da N5,000 da bankuna suka yi.
“Ma’aikatan POS suna iƙirarin cewa suna siyan kuɗi daga bankuna da gidajen mai, don haka suke sayar wa jama’a domin su ci gaba da kasuwanci.
“Wannan rashin adalci ne, ko da tare da kuɗi a cikin asusun ku, ba za ku iya samun damar samun kuɗi ba. Lamarin ya zama wanda ba za a iya jurewa ba,” inji shi.
Miss Uduak Enoch, wata ma’aikaciyar jinya, ta ce da misalin ƙarfe 5:00 na safe ta farka ta yi layi a na’urar ATM domin samun kuɗi.
“Har ila yau, babu tabbacin cewa za ku sami kuɗi. Mafi akasarin na’urar ATM ba sa fitar da sama da Naira 10,000,” inji ta.
Wani mai sana’ar POS mai suna Omini Mike ya ce ya biya kuɗin ne saboda ya sayi kuɗi daga gidajen mai da manyan kantunan mai.
“Don haka lokacin da kuka ga ina ƙara caji akan ma’amaloli, ba laifi na ba ne, ina buƙatar samun riba, na saka hannun jari don samun kuɗin,” in ji shi.