Ƙarancin takardun kuɗin Naira

Ƙarancin Naira na cigaba da shafar ’yan Nijeriya da ’yan kasuwa duk da cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bin umarnin da Kotun Ƙoli ta yanke na cewa tsofaffin takardun kuɗin Naira za su ci gaba da yaɗuwa a kasuwa har zuwa ƙarshen shekara. Taɓarɓarewar sha’anin kuɗin dai na ci gaba da ƙaruwa duk da umarnin da CBN ya baiwa bankuna na ci gaba da fitar da tsoffin takardun kuɗi kamar yadda Kotun Ƙoli ta yanke.

Wani bincike da masana da ƙungiyar masu tunani na CBN suka yi na sake fasalin manufofin Naira da kuma tasirinsa ga ’yan ƙasa da tattalin arzikin ƙasar, ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya tsaya cak tare da asarar da aka kiyasta ya kai Naira tiriliyan 20 sakamakon sama da kashi 70 cikin 100 bisa taɓarɓarewar sha’anin kuɗi da CBN ta yi. Wani rahoto da cibiyar bunƙasa masana’antu masu zaman kansu ta fitar, ya nuna cewa ƙarancin kuɗaɗen da ake fama da ita ba kawai ta gurgunta harkokin tattalin arziki ba, har ma ya zama babbar barazana ga rayuwar ’yan Nijeriya.

Bayan haka, akwai alamun rugujewar tsarin biyan kuɗi a duk dandamali. Alƙaluman da hukumar kula da hada-hadar kuɗi ta Nijeriya (NIBSS) ta fitar sun nuna cewa, yawan amfani da na’urar biyan kuɗi ko tsarin biyan kuɗi ta ‘e-payment’ ya samu qaruwar kashi 41.29 cikin 100 a duk wata, yayin da hanyoyin biyan kuɗi da aka yi amfani da su a watan Fabrairu sun kai miliyan 901.46. sau, daga sau miliyan 638 a watan Janairu. Duk da ƙaruwar amfani, jimillar darajar hada-hadar kuɗi ta faɗi a cikin watan Fabrairu, wanda ke nuni da cewa adadin ma’amalolin da suka gaza ya ƙaru saboda rashin kyawun hanyoyin sadarwa. Wannan ya saɓa wa tsammanin cewa manufar sake fasalin Naira zai ƙara hada-hadar biyan kuɗi ta yanar gizo a ƙasar.

Wani abin ban mamaki shi ne duk da ƙarancin kuɗin da ake samu, kasuwar sayar da kayayyaki ta ƙaru daga Naira biliyan 807 a watan Janairu zuwa Naira biliyan 883.4 a watan Fabrairu, yayin da musayar wayar salula ta qaru daga sau miliyan 108.14 a watan Janairun 2023 zuwa sau 183.69 a watan Fabrairu.

Wannan shi ne saboda yawancin abokan ciniki sun koma yin amfani da tsarin biyan kuɗi ta e-pay a cikin wannan lokacin tun lokacin da yawancin bankunan suka rufe rassansu saboda tsoron hare-hare, kuma masu gudanar da kasuwancin POS sun ba da kuɗaɗen hakan don cajin babbar hukuma kan hada-hadar kasuwanci.

Duk da haka, ƙimar ciniki ta ƙaru kaɗan da kashi 7.88 daga Naira tiriliyan 2.37 a watan Janairu zuwa N2.56trillion a cikin Fabrairu. Wannan ya yi nuni da irin mummunan halin da yawancin ‘yan Nijeriya da ‘yan kasuwa ke ciki sakamakon matsanancin ƙarancin kuɗi. Ko shakka babu manufar sake fasalin tsarin Naira na da wasu fa’idoji na tattalin arziki kamar inganta hada-hadar kuɗi, tara kuɗi da jabun kuɗaɗen haram, musayar kuɗi da wawure dukiyar ƙasa da kuma magance maƙudan kuɗaɗe a wajen tsarin banki.

Duk da haka, rugujewar manufofin ya zama bala’i, tare da tasiri ga tattalin arzikin ƙasa. Babu shakka Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Ƙasar, CBN, sun raina ɓangaren samar da kuɗi, wanda a yanzu haka ke haifar da cikas ga tattalin arziki da kuma asarar kayayayyaki. An samu rashin ingantaccen sadarwa daga hukumar kuɗi (CBN). Har ila yau, lokacin aiwatar da manufofin, tun da farko, bai dace ba kuma ba zai yiwu ba. Muna kula da cewa ba a yi la’akari da wannan manufar a hankali ba.

Ya kamata CBN da bankunan kasuwanci su gaggauta zaukar mataki kan samar da isassun tsofaffi da sabbin takardun kuɗi. Cewa taɓarɓarewar kuɗi ta kai ga wannan rikici wani ɓangare ne na Gwamnatin Tarayya da CBN da kuma bankunan kasuwanci tun farko ba su da gaskiya da hukuncin Kotun Ƙoli har sai da abubuwa suka kusa ƙarewa.

Akwai buƙatar wayar da kan jama’a cewa tsohon takardun Naira ya ci gaba da yaɗuwa a gari har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023. Hakan ya zama dole don dakatar da qin amincewa da tsofaffin takardun da ‘yan kasuwa da masu sufuri ke yi. Dogayen layukan sun kasance a banki daban-daban wajen na’urori masu sarrafa kansu (ATM) yayin da abokan ciniki ke shan wuya wajen cire kuɗi.

’Yan Nijeriya sun shiga mawuyacin hali a ’yan kwanakin nan. Baya ga matsi na kuɗi, ƙarancin man fetur ya kasance wata matsala da ‘yan ƙasar ke fama da shi sama da watanni shida yanzu.

Magance waɗannan al’amurra ya zama da amfani don kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da rushewar doka da oda. Don haka ya zama wajibi gwamnati da CBN su haɗa hannu da kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati don ganin an cimma manufar sake fasalin kuɗin Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *