Daga AMINA YUSUF ALI
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, ƙarar da jam’iyyar PDP ta shigar don neman soke Tinubu daga takarar shugabancin ƙasar nan a 2023, da ita da wasan yara duk ɗaya ne. Domin ba wani abu ne da ya kasance barazana ga jam’iyyarsu ta APC ba.
Jam’iyyar PDP dai ta shigar da wata ƙara a kan hukumar zabe ta ƙasa INEC, da ɗan takarar APC Bola Tinubu, da Dakta Peter Obi a kan yadda suka sauya abokan takararsu na wucin gadi a yayin kuma da suke yin takara da wasu abokan takarar daban.
A cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Arise TV ranar Lahadi, Adamu ya bayyana cewa, su fa dokokin wannan ƙasar fa a bayyane suke. Duk shaqiyyancin da mutum zai yi, dole akwai dokar da za ta taka masa burki.
Haka kuma a cewar sa, duk wani ɗan takara da APC ta fitar sai da ta yi zaɓen cikin gida kafin ta cimma matsayar zaɓar sa.
Adamu ya ƙara da cewa, a shari’ance APC tana da hurumin da ya ba ta damar zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na wucin gadi wanda zai ba ta damar zaven sahihin ɗan takararta a tsanake. Kuma dokar INEC a cewar sa ita ta ba da wannan dama. “Da ba mu da wannan hurumin ma a shari’ance ma ba za mu fara ba”. A cewar sa.
Amma a cewar sa, tunda PDP sun garzaya kotu, to shi bai ma ga abin ta da jijiyar wuya a ciki ba. Sai a jira hukuncin kotu kawai. Don haka a cewar sa duk abin ba fa na ɗaga hankali ba ne.