Ƙarfafa ɓangaren kasuwanci ne mafita ga samar da aiki a Nijeriya – Malagi

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa ingantaccen fannin kasuwanci zai taimaka gaya wajen samar da guraben aiki a Nijeriya.

Ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ministocin Shugaba Bola Tinubu kuma mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja.

Malagi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa don tantancewa a matsayin minista.

Da yake jawabi, Malagi ya shawarci Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa (NBC) da ta bi diddigin lasisin gudanarwar da aka bai wa masu son kafa gidajen yaɗa labarai a faɗin ƙasa.

Game da yadda ɓangaren ‘yan kasuwa zai taimaka wa gwamnati wajen magance matsalar rashin aiki a ƙasa, Malagi ya ce domin cim ma wannan ƙuduri ya zama dole a samar da yanayi mai armashi ga masu ruwa da tsaki a fannin don haƙa ta cim ma ruwa.

Ya ce zai kyautu a saka wani ɓangare na Naira tiriliyan ɗaya da gwamnati ta tara sakamakon cire tallafin mai cikin harkar kasuwanci don samar da aikin yi ga ‘yan ƙasa.

“Mu ƙarfafa ɓangaren kasuwanci, ta haka za mu iya samar da guraben aiki ga matasanmu da ba su da aiki.

“Babu yadda za a yi gwamnati ta iya ci gaba da ɗaukar mutane aiki – ina ganin an wuce wannan zamanin inda ake tunanin gwamnati za ta bai wa kowa aiki a Nijeriya, zamanin ya shuɗe,” in ji Malagi.