Ƙarin abokai sun shiga shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”

Daga CMG HAUSA

Yau Talata, hukumar zurfafa gyare-gyare a gida da buɗe ƙofa ga waje ta ƙasar Sin, ta shirya wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar Meng Wei ta yi bayani cewa, ya zuwa yanzu, Sin ta ƙulla yarjejeniyoyin haɗin kai fiye da 200 ƙarƙashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, tare da ƙasashe 149 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 32.

Rahotanni na cewa, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, ƙasar Sin ta ƙulla yarjejeniyoyi da ƙasashen Nicaragua da Syria da Argentina da Malawi da sauransu, ƙarin abokai dake amincewa da shawarar.

A farkon rubu’in bana, jiragen ƙasa sun yi zirga-zirga tsakanin Sin da Turai sau 3630, kana yawan sunduƙan da aka yi jigilarsu, ya kai dubu 350, waɗannan alƙaluma biyu sun ƙaru da kashi 7% da 9%, adadin jiragen ƙasa da aka yi amfani da shi a wata ɗaya, ya kai fiye da dubu a cikin watanni 23 a jere da suka gabata. Matakin da ya ba da tabbaci ga tsare-tsaren samar da kayayyaki a duniya.

Mai Fassarawa: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *