Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Zamfara ta yi alƙawarin shiga yajin aikin da ƙungiyar NLC ta ƙasa ta shirya shiga a faɗin ƙasa.
Da yake jawabi a wajen taron da suka shirya ranar Litinin, Shugaban NLC na jihar Zamfara, Sani Haliru, ya ce an kammala duk wani shiri da tuntuɓar juna domin samun nasarar yajin aikin a jihar.
A cewarsa, ma’aikatan jihar Zamfara na bayan shugabancin NLC ta ƙasa wajen zanga-zangar nuna rashin yarda da cire tallafin man fetur.
Ya ƙara da cewa, “Mun lura da sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a baya-bayan nan game da cire tallafin man fetur ya ta da ƙura a ƙasar.”
Don haka shugaban NLC ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta duba lamarin cire tallafin na fetur.