Ƙarin girma: Hukumar ’Yan Sanda ta yi wancakali da Magu

…Biyo bayan rahoton Ayo Salami, an ciyar da ’yan sanda da dama gaba

Daga NASIR S. GWANGWAZO, a Abuja

Hukumar Kula da Aikin ’Yan Sanda a Nijeriya (PSC) ta yi wancakali da batun ƙara wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Ta’annatin Kuɗi da Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ibrahim Magu, biyo bayan rahoton Kwamitin Mai Shari’a Ayo Salami, wanda ya zargi Magun da aikata ba daidai ba a lokacin da ya ke shugabantar hukumar ta EFCC.

Kazalika, Hukumar PSC ta yi ƙarin girma ga manyan ‘yan sanda guda uku zuwa muƙamin Muƙaddashin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa (DIGs), yayin da aka ciyar da wasu kwamishinoni guda huɗu zuwa muƙamin Mataimakin Babban Sufeton (AIGs).

Wannan ya biyo bayan zaman da hukumar ta yi ne a ranar Talata da Larabar da suka gabata a zamanta karo na 12 ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Musiliu Smith, wanda tsohon Babban Sufeton ’Yan Sandan Ƙasar ne.

Kazalika, a zaman, an kuma amince da yi wa jami’ai 35 ƙarin girma zuwa muƙamin Kwamishina, jami’ai 52 kuma zuwa muƙamin Muƙaddashin Kwamishinan ’Yan Sanda da 46 zuwa matakin Mataimakan Kwamishinan ’Yan Sanda.

Haka nan hukumar ta amince jami’ai 10 su samu ƙarin muƙami zuwa Babban Sufurtanda, 17 zuwa matakin Sufurtanda, yayin da 139 kuwa zuwa muƙamin Muƙaddashin Sufurtanda, inda kuma Tara suka samu ƙarin girma zuwa matakin Mataimakin Sufurtandan ’Yan Sandan Nijeriya.

Sai dai kuma duk wannan shagali da rahusa da garaɓasa da a ke yi a Rundunar ’Yan Sandan ta Ƙasa, Malam Magu bai rabauta ba, inda Hukumar ta PSC ta ce, ta na jiran shawari daga ofishin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya da ofishin Babban Sufeto Janar.

Masu lura da al’amuran yau da kullum da kuma manazarta kan harkokin cin hanci da rashawa su na nasabta wannan ƙememe da yadda rahoton kwamitin bincike da Fadar Shugaban Ƙasa ta kafa kan yadda Magu ya tafiyar da EFCC a zamaninsa ƙarƙashin jagorancin tsohon Alƙali Ayo Salami, ya zarge shi da aikata ba daidai ba kuma ya bayar da shawarar a gurfanar da shi a gaban kuliya baya ga sauke shi daga muƙamin shugabancin hukumar ta EFCC.

Ganin yadda da fari aka bayar da rahoton cewa, Mista Magu na daga cikin waɗanda za a yi wa ƙarin girma, hakan ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar kan gaskiyar aniyar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. To, amma janye sunansa daga cikin waɗanda za a ƙara wa girma, za a iya cewa, ya kwantar wa da manazarta hankali tare da dawo da kyakkyawan zaton da ake yi wa Shugaba Buhari a idanunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *