Ƙarin kuɗin haraji: ‘Yan kasuwa sun koka da hukumar Kwastom

Daga AMINA YUSUF ALI

‘Yan kasuwa sun koka a kan yadda a kan yadda hukumar Kwastam ta yi ƙarin kuɗin harajin ba-zata. 

Hakan ya biyo bayan ƙarin ba-zata na kuɗin harajin shigo da kaya da hukumar Kwastam (NCS) ɗin  ta yi a kwanakin baya. Abinda ‘yan kasuwar suka ce yana kawo musu cikas wajen gudanar da kasuwancin nasu.

Wasu ‘yan kasuwa da suka zanta da jaridar ‘Vanguard News’ cewa, ba wai cikas ƙarin kawai ya jawo a kasuwancinsu ba har naƙasu ya kawo a cikin kasuwancinsu da ribar da suke sa ran samu. 

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar masu dakon kaya daga ƙasar waje, Reverend Jonathan Nicole, ya bayyana cewa, ya ce sam wannan ƙarin harajin ba zai haifar da ɗa mai ido ga ‘yan kasuwa ba. Domin wannan ƙarin zai iya haifar da a samu ƙarin kuɗin shigo da sunduƙin kaya wato ‘clearance’.

Kuma a cewar sa hakan zai ƙara kawo hauhawar farashin kaya a kasuwa abinda zai iya kai wa ga samun karayar tattalin arzikin ƙasa da tsadar rayuwa. Wannan shi ne dalilin da ya sa sam masu dakon kayan ba sa murna da wannan ƙari, a cewar sa. 

Da yake nasa jawabin, shugaban ƙungiyar shugabannin hukumar kwastomomi ta ƙasa (NCMDLCA), Lucky Amiwero, ya ce ƙarin zai ƙara jefa ‘yan Nijeriya a cikin mawuyacin hali. Domin a cewar sa, ƙasar ta dogara kacokam ne da kayayyakin da ake shigowa daga ƙasashen ƙetare. 

Ya ƙara da cewa, in dai aka tafi a haka, watarana sai sayayar abu ta gagari talakan Nijeriya. Domin tsadar rayuwar za ta wuce duk yadda ake tsammani. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *