Ƙarya fure take ba ta ’ya’ya

Daga AMINA XU

Wasu abokai sun aiko min sako cewa, BBC ta ba da labarai game da ƙasar Sin cewa, tana cin zalun musulmai da tilasta musu aiki a yankin Xinjiang…….Abin baƙin ciki ne ganin yadda Intanet ke bunƙasa matuƙa a karni na 21, amma wasu kafofin yaɗa labarai sun zama wani dandali na yaɗa jita-jita da labarai marasa tushe.

A haƙiƙa, kafofin yada labarai na ƙasashen yamma sun sha yaɗa irin waɗannan ƙarairayi game da ƙasar Sin da ma sauran wasu ƙasashe, don neman shafa musu baƙin fenti.

Hausawa kan ce, ”Gani ya kori ji”, ba za a kai ga gano gaskiya ba, idan an saurari wata kaɗai ba. Waɗannan ƙarairayi da kafofin yaɗa labarai na yamma suke watsawa, sun yi kama da hancin Pinocchio, wani mutum mutumin a cikin almarar ƙasashen yamma, wanda hancinsa ya yi tsawo saboda ƙaryar da yake bazawa. Ba shakka, Karya fure take ba ta ’ya’ya.

Mai zane: MINA