Ƙarya ita ce musabbabin yawan mutuwar aure (2)

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Ci gaba daga makon jiya.

Rashin aikin yi:

Rashin aiki ga matasa ya daɗa taɓarɓara abubuwa. Saboda samarin na son auren amma ba su da abun auren a hannunsu. Sannan tsarabe-tsarabe na aure ya daɗa haddasa koma-bayan aure, dole mata su yi yawa.

Da za a taru, daga matan har mazan a sauƙaƙa wa rayuwa, da an ji da]i. To kowa ya ci buri. Mata sun ci burin auren mai gida da mota da akwatuna da yawa. Su ma mazan sun ci burin sai ‘yar wani ƙusan, ko mai faɗa a ji zai aura. Ko don ya samu kuɗi ko jari.

Rayuwa ba za ta tafi da ƙarya ba. Iyaye ma suna da hannu a ciki. Tunda yaro zai zo da wannan batun, amma suna gani sai su sa musu ido ko su ce gaskiya ne. Meye amfanin auren da ba riba? Ya zama ma ba alherin auren ake nema ba, abun duniya ake so. Dole kuwa mu yi ta ganin yaranmu a gabanmu, tunda ba don Allah ake yin auren ba. Wasu ma yanzu kayan auren ake arowa na gani, na fa]a a kai gidan su yarinya ana ta murna ta yi goshi. Sai an kai ta gidan miji ya ƙwace kaya ya maida wa mai su. Ko a yi Aron gidan da za ta zauna ana murna ta samu gida na hutu. Kwana biyu, sati ɗaya, maigida zai zo ya amshi gidansa. Ba abunda yanzu ba ya faruwa a cikin wannan rayuwar. Lallai iyaye su yi hattara kada son yaranmu ya rufe mana ido, mu zo muna da mun sani daga baya. Wallahi matsalar da ta Kunno Kai yanzu, yaran ba su da aikin yi. Ba sana’a, kawai sai buga-buga. Karatun ma wasu ba su yi ba, amma suna samun canji a hannu, sai su ce aure. Iyaye kuma ba dubaiyya ba komai, sai a tashi aure. Daga baya fitina ta Kunno a yi baram -baram. Duk soyayyar da aka yi, sai ta tashi kamar ba a yi ba. Sai tsantsar ƙiyayya ta danne zaman so da ƙauna da aka yi a da.

Kowanne jinsin aka taɓa, yanzu kowa na da laifi. Kawai mu dogara da kanmu, mu yi kokarin zaɓa wa yaranmu gidan aure na gari.

Ita rayuwa dai ‘yar dubaiyya ce. Yadda ka ɗauke ta, haka za ta zo maka. Saboda haka, mu yi karatun ta-nutsu, mu yi haƙuri mu zauna gidan mazajen mu lafiya. Kada mu yi hange-hange mu kashe aurenmu, ko na yaranmu, mu zo muna cizon hannu.

Zawarci ba abun gudu ba ne idan ya zo wa mata. Mu yi musu fatan alheri. Su kuma, su tsare martabarsu ta mata, Iyayen wasu ne, har Allah ya fiddo musu na gari. Don ba a rasa na gari. Maza a ji tsoron Allah. A duba, a daina yaudarar mata. Idan ba aure ne a ranka ba, to kada ma ka fara nema, balle har ka cutar. Idan kuma shi ne, to a yi fatan a arziki, ba tsiya ba. Sai Allah ya duba mu. Zawarci ƙaddara ne, ba wai abun gudu ba ne. Don haka daga matan, har mazan mu sa Allah cikin zukatanmu. Amma ina! Yaudara ce ta yi yawa, to fa za a yi da-na-sani.

Yara amana ce a gurin iyaye. Kada a biye musu, su faɗa halaka. A nuna musu yadda sha’anin rayuwar yau take.

Aure:

Idan aka samu namiji mai aure-aure, shi ma hatsari ne a rayuwar yara mata. Saboda kawai tinƙaho yake yana da ku]in ajiye duk matan da ya so. Ya manta da dukiya da yara ba a musu mugunta. Yadda ka yi wa yaran wasu, ka tuna kai ma fa naka za a iya yi musu don baka wuce ba. Mutum ya yi ta faman tara mata da yara yana saki, ko anan ma ai ya ba wa zawarawa gudunmowar tagaiyyara rayuwarsu. Tunda za ka aura ka saki, gobe ma haka. Ga mutuwar aure, ga tara yara barkatai. Kenan babu maganar tarbiyya. Dole ko a samu fitunannu cikin gidanka don sun yi yawan da ba a iya basu kulawa. Kowacce mace nata za ta kula. Su waɗancan da aka saki iyayensu ,ko oho. Ka ga ka ba da gudunmowar taɓarɓarewar rayuwar gidanka.

Don Allah mu nutsu, mu duba. Ita fa mace abar dubaiyya ce. Don me za ka aura ka kasa riƙewa? idan ka san ba za ka iya ba, sai ka bar ta, wani ya aura. Amma idan kuɗi sun rufe maka ido, sai ka baɓa rayuwar gidanka.

Haƙurin nan dai da a ke cewa mace ta yi, to dole ne fa ta yi. Saboda sha’anin rayuwa sai an ciza. Kada ki yi la’akari da kanki. Ki yi duba ga zuri’arki. Ko don su mace ta haƙura ta zauna a ɗakinta.

Za mu tsaya a nan sai sati na gaba idan Allah ya sa muna raye. Abin da muka yi ba daidai ba, Allah ya gyara mana. Wanda muka yi daidai, Allah sa masa albarka. Shawara, gyara, ko neman shawara, duk ƙofarmu a buɗe ta ke. Ku kasance da mu a kullum cikin Jaridar Manhaja ta kamfanin jaridu na Blueprint. Wassalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *