Ƙarya ku ke, mutum 20 su na hannun ƴan bindiga – Majalisar Neja ga sojoji

Majalisar Dokokin Jihar Neja ta tabbatar da sace mutane fiye da 20 a cikin motoci biyar da suka shiga hannun ‘yan bindiga a hanyar Mariga-Kontagora. Kakakin majalisar, Barista Abdulmalik Sarkin-Daji, wanda ke wakiltar mazaɓar Mariga, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, inda ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun tare hanya a tsakanin ƙauyen Baban-Lamba da Beri a ranar Alhamis.

Sarkin-Daji ya yi wannan bayani ne don mayar da martani ga sojoji, bayan da suka musanta rahoton da ke cewa ‘yan bindiga suna fakewa a wajen horonsu da ke Kontagora, wanda kuma yake kusa da yankin Mariga. Kakakin ya ce al’ummomi sun sha kai kuɗin fansa ga ‘yan bindigar a cikin dajin da ya ke kusa da sansanin horon sojoji na Kontagora, wanda ‘yan bindigar ke amfani da shi wajen ɓoye waɗanda suka sace.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa mazauna yankin da aka sako bayan an biya kuɗin fansa sun shaida wa iyalansu cewa wurin da aka ajiye su bashi da nisa da sansanin sojoji. Haka kuma, waɗanda aka sace a ranar Alhamis an ɗauke su zuwa wannan daji, inda aka yi kira ga sojoji da su bincika gaskiyar lamarin tare da kawo ƙarshen ‘yan bindigar a wannan wuri.

“A matsayinmu na wakilan al’umma, muna sauraron ƙorafin jama’armu kafin mu gabatar da batutuwan da suka shafe su a majalisa. Ba ma kokarin raina ƙarfin sojoji wajen yaƙar ‘yan ta’adda, amma ba daidai ba ne su yi watsi da ƙorafin al’umma,” in ji Sarkin-Daji. Ya kuma bayyana cewa ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya da hukumomi su ɗauki matakin da ya dace domin kare al’ummar yankin.

A ƙarshe, Sarkin-Daji ya yi kira ga sojoji da su ɗauki rahotannin da ake bayarwa da muhimmanci tare da yin aiki da sahihan bayanai domin fatattakar ‘yan bindiga daga yankin. Ya bayyana cewa, a matsayin sojoji, wajibi ne su kare rayukan jama’a kuma za su ci gaba da faɗin gaskiya don isar da saƙon halin da al’ummar yankin ke ciki ga gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.