Ƙarya tsakanin ma’aurata

Daga AMINA YUSUF ALI

A wannan mako za mu yi bayani a kan wani abu da ya zama ruwan dare a gidajen aure, kuma ya zama jiki har ma ana ganinsa ba wani laifi ba ne sosai. Domin kusan dukkan ma’aurata suna yi wa junansu ƙarairayi.

Mecece ƙarya?

Da farko dai ƙarya wani zance ne da ake yi don a yaudari wani ya zaci abinda aka faɗa gaskiya ne. Wato ko dai a yi wa labar ƙari da kwaskwarima, ko kuma ma gabaɗaya ba labarin kawai an ƙirƙire shi ne. A musulunce ƙarya dai tana matsayin kaba’ira wato ɗaya daga cikin manyan laifuka da Allah ba ya yafe su. Amma wasu suna ganin ba kowacce nau’in ƙarya ba ce zunubi a gurin Allah.

Domin wasu suna ganin ƙarairayin da ma’aurata suke yi wa junansu sun fi gaskiyar amfani da taimakawa wajen kawo musu zaman lafiya. Amma waɗanne irin ƙarairayi ma’auratan ke yi wa juna?

Ire-iren ƙarairayin da ma’aurata suke yi wa junansu?

Magana mai harshen damo ko rashin ba da amsa kai tsaye a kan wata magana.

Nau’in ƙarya na biyu shi ne, zuzuta ko ƙarin gishiri. Misali miji ya dinga nuna wa matarsa yana samun kuɗi fiye da zatonta, ko kuma idan ya sayi abu ya yi ƙari a kai don ya burge ta. Ko kuma ita matar idan savani ya afku ita da kishiya ko dangin miji ta yi ƙarin gishiri a labarin da ya afku don ta samu goyon bayansa. Ko kuma idan miji ya siyo abu ba ki ga kyansa ba, amma ki yi ta kwaɗa abun da nuna cewa abun nan yana da kyau.

Akwai ƙaryar da ake yi kuma don ƙasƙantar da abu a nuna wa abokin rayuwa cewa abu kaza ba shi da muhimmanci. Misali mace ko namiji suna matsananciyar damuwa ko rashin lafiya. Amma sai a nuna wa abokin rayuwa kada ya damu ba wata matsala ba ce babba. Amma kuma su kaɗai suka san halin da suke ciki.

Rashin ba da cikakken bayani a kan wani abu. Ko kuma ta hanyar ɓoye wani bayani wanda ba sa so abokin rayuwarsu ya sani.

Ƙananan ƙarairayi a kan al’amuran yau da gobe. Misali ta ce ya siyo mata abu idan ya je kasuwa. Shi kuma ba zai iya ce mata rashin kuɗi ne ya hana shi ba. Saboda za ta raina shi. Kawai sai ya ce mata, ya mance. Ko ya ce ya rasa a kasuwa.

Ƙarya ta kai tsaye. Wannan ita ce ma fi munin ƙaryar da ma’aurata za su yi wa junansu. Ita ce wacce da wuya ta iya yafuwa. Ko da an yafe ɗin kuma, sai ka ga an kasa dawo da yarda da juna. Misali kafin a yi aure a ɓoye wa abokin rayuwa zahirin yadda yawan mata ko ‘ya’ya. Misali bazawara ce da ‘ya’ya biyu ko ɗaya, shi kuma ya aura a matsayin budurwa. Kun ga wannan ƙarya da wuya a iya yafewa. Idan ba a ci sa’a ba ma, auren ya watse.

Idan muka ɗauke zancen ma’aurata, mu duba cewa ma gabaɗaya me ya sa mutane suke ƙarya? Za mu ga ba zai wuce ɗaya daga cikin waɗannan dalilai ba masu zuwa:

Ana yin ƙarya a samu rabauta da wani abu. Ko kuma don tsoron kada a hukunta mutum a kan wani laifi da ya yi. Ko kuma don qara wa abinda aka faɗa armashi yadda zai fia jan hankali.

Bayan haka, ana yin ƙarya domin a vata wani a wajen wasu mutane, ta hanyar yi masa sharri da wasu abubuwa da za su zubar masa da mutunci a idon waɗancan mutanen. Sannan kuma akwai mutanen da aka halitta da ɗabi’ar ƙarya. Duk wata maganarsu sai sun sako ƙarya a cikinta saboda sabo da yi.

Haka rashin tsoron Allah da rashin tarbiyya suna sa wa mutum ya zama maƙaryaci. Wanda idan mutum yana yin ƙaryar yau da gobe, ko ya aka yi ƙoƙarin gano shi, sai ya yi wata ƙaryar ya lulluɓe waccan ta farkon da ya yi. Daga haka sai a ga mutum ya zama ƙasurgumin maƙaryaci. Duk da dai wasu kuma gadar ta suke yi a wajen iyaye ko su koya wajen abokan da suke tare da su.

Hakazalika, mutane suna yin ƙarya saboda su ƙara ƙima su yi burga a cikin mutane. Hakan a tunaninsu zai ƙara musu kwarjini. An fi yin ƙaryar arziki da ta muqami. Duk da dai ana yi ƙaryar ilimi wani zubin, amma da sauri ake ɗago mutum idan ya yi. Domin ba ya vuya.

Amma su ma’aura irin tasu ƙaryar suna yinta domin ɓoye wani bayani daga abokan rayuwarsu. Suna ɓoye-ɓoyen ne don son samun soyayya ko mutuntawa ko yardar abokin rayuwarsu. Wani lokacin ma har da son a zauna lafiya ko kare wani aibi ko abin kunyarsu daga abokin rayuwa. Saboda akwai wasu sirrika da idan abokan rayuwarsu suka gano, zaman lafiya yana iya yin wahala a gidan.

Duk da dai wasu suna ganin cewa, da wahala a samu ma’auratan da suke faɗar gaskiya ƙeƙe da ƙeƙe ga juna. Wasu ma suna ganin yin hakan rashin dabara ne.

Tun daga farkon aure ko a nema ma’aurata suke fara yi wa juna ƙarya. Kowa a cikin ma’auraan ƙoƙari yake yi ya nuna shi na kirki ne. Bayan an yi aure kuma, za a ɗan cigaba da yi wa juna ƙarya a satittika ko watannin farkon auren. Misali idan tana Amarya ko girki bai daɗi ba za a ce ya yi daɗi, kawai don ta ji daɗi. Haka kwalliyarta za a yaba ko da ba ta yi ɗin ba. Haka ita ma duk wani abu da ta gaya maka lokacin kana nemanta za ta yi ta kaffa-kaffa. Sai idan zama ya yi zama ne wasu abubuwa suke bankaɗuwa kuma idan ba a ci sa’a ba, abin ya ƙi daɗi.

Haka ma’aurata suna yi wa juna ƙarya domin su samu aurensu ya tabbata. Misali kamar namijin da zai yi ƙaryar ba shi da mata kuma sai an yi auran a gani. Ko kuma ya ce matar ba ta da wani tasiri ba ta kula da shi. Ko kuma rashin lafiya a voye. Irin wannan ƙaryar dole fa za ta fito. Amma shi tunda ya yi ta don ya samu buƙatarsa ta biya, zai ga ba wani abu ba ne.

Ko kuma idan a tarihin rayuwarsa ya rabu da mata da dama, sai ya nuna mata cewa, abinda ya raba shi da sauran matan duk laifinsu ne. Ya nuna dai su suke muzguna masa. Alhali shi ne mai wannan halin na rashin haƙurin zama da su.

Ana yin ƙarya don tunanin ɓoye gaskiya ga wanda ake tare, miji ko mata zai kawo zaman lafiya. Amma da zarar an yi ƙaryar farko, sai an yi ta yin wasu don rufe ta farko. Daga ƙarshe kuma sai rayuwar auren ta zama ba komai a cikinta sai ƙarya.

Haka akwai miji ko matar da su suke janyowa abokin zamansu ya zama maƙaryaci. Ta hanyar yadda suke karvar gaskiya idan an kawo musu ita. Misali mace ta faɗa wa miji gaskiyar zance sai ya hayayyaƙo mata da fushi da faɗa da sababbi. To daga wannan ranar ya koyar da ita cewa, shi ba mutumin da za a yi wa zancen gaskiya ba ne ya fahimta. Sai ta ɗauki ɗabi’ar yi masa ƙarya, daga nan kuma.

Haka matar da mijinta zai yi wa kishiyarta abu ko danginsa ta nuna hassada a kai. Ita ma nan gaba ta koya masa ƙarya da ɓoye-ɓoye.

Amma ni a nawa ƙaramin tunanin, ita aminci da yarda su ne aure da zaman tare. Kowacce alaƙa idan za a ƙulla ta ana buƙatar waɗancan abubuwa guda biyu. Ballantana alaƙar aure da ake fatan idan an gina ta har muddin rayuwa?
Haka sannan masu ƙarya domin a aminta da su a aure su. Ina amfanin baɗi ba rai?

A kowanne lokaci fa gaskiyar nan dai da muke gudu sai ta ɓullo. Kuma mun san ɗacinta wane mur! Daga lokacin da ta bayyana shikenan rigima ta ɓulla. Sai zargi, sai rashin yarda a tsakanin juna. Sai zubewar ƙimar wanda ya yi ƙaryar a idon abokin zamansa.

Haka ba ka buƙatar ka yi wa kowa ƙarya ya so ka. Mai sonka zai so ka duk da aibunka. Haka idan mutum mijinki ne ko Allah ya ƙaddara matarka ce, to ba makawa sai ka aure ta ko sai kin aure shi. Don haka gara a fito a faɗa wa juna gaskiya da gaskiya. Domin aure zama ne ba na ƙare ba. Kuma abinda wani ya qi ka don shi, wani kuma don shi zai so ka. Haka rayuwa take.

Amma akwai wasu lokutan da idan ka faɗi gaskiyar kuma za ta jawo ruɗani da tashin hankali. A musulunce ma an yarda ka yi ƙaryar a wannan halin. Misali wata ƙanwar tsohon saurayinki ta kawo miki ziyara. Mijinki ya tambaye ki wacece? kika faɗi gaskiya kinga ai da matsala. Ko kuma idan kika tambayi mijinki da ke da kishiyarki wa ya fi so? A nan ma idan ita ya fi so, kuma ya faɗa ai ba za ki ji daɗi ba.

Amma fa idan ba irin wannan yanayi ba, ƙarya haramun ce kuma yaudara ce da cin amana. Kuma a zub da ƙima idan gaskiya ta yi halinta.
Ma’aurata su sani amana da yardar nan suna da matuƙar muhimmanci a tsakaninsu. Gara ka faɗi gaskiya komai ta ja maka ka biya. Kamar yadda marigayi Sa’adu zungur ya faɗa a wata waƙarsa. Ƙarya duk yadda ka kai ga dabara da iya ɓoye ta, yau da gobe fa ta fi ƙarfin wasa. Don hala faɗar gaskiya ga abokin zama ta fi ƙaryar da za a yi masa ya ji daɗi a ƙanƙanin lokaci.

An san da ba wanda zai ce yana da gaskiya koyaushe. Fadar gaskiya ma fi yawan lokuta ya fi. Na san wasu suna cewa gudun zuciya yake sa su yi ƙarya. Amma bai kyautu a fifita fushin wani a kan na Allah ba. Kuma ɓoye sirri yana ba wa shaiɗan galaba a kan ma’aurata. Bissalam. Sai mun haɗu a mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *