Ƙasa mafi arziki a Turai ta tsunduma cikin karayar arziki

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙasa mafi arziki a Turai, wato Jamus ta tsunduma a cikin hakin matsin tattalin arziki.

A wani rahoto da aka tattara a ofishin tattara bayanai a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana cewa, gabaɗaya ƙarfin tattalin arzikin ƙasar (GDP) ya ragu zuwa kaso 0.3 a cikin watanni huɗun farkon shekara.

Jamus, ƙasar da ta fi kowacce qasa a arziki a Turai, kuma ta huɗu mafi arziki a duniya bakiɗaya, ta tsunduma cikin matsin tattalin arziki a watanni huɗun farko na shekarar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, tattalin arzikin ya yi ƙasa sosai a watanni huɗu a jere. Yayin da aka samu haka kuwa, akan samu faɗuwar tattalin arziki.

Amma a ɓangaren kasuwanci kuma da kayan aiki da na’urori sun ƙaru da kaso 3.2 daga watanni huɗu na shekarar da ta gabata ta 2022, zuwa farkon shekarar 2023.

Idan taahin farashin ya ɗore kuma, zai zama ya yi nauyi ga tattalin arzikin ƙasar a farkon shekarar, inji jami’in tattara bayanan.

Kuma a cewar sa, kasancewar Jamus babbar cibiyar tattalin arziki, hakan zai iya gadarwa ga Babban Bankin Turai ya qara tsananta adadin kuɗin ruwa na bankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *