Ƙasar Benin ta lallasa Najeriya a wasan neman gurbin cin kofin duniya

Ƙungiyar kwallon kafa ta super eagles tayi rashin nasara a wasan neman gurbin cin kofin duniya a hannun takwararta ta ƙasan Benin wanda tsohon mai horar da super eagles din Gernot Rohr ke jagoranta. In da aka tashi wasan 2-1.

Da wannan wasan Najeriya na da maki uku cikin wasanni huɗu. za a dawo wasa na biyar a cikin watan Maris din shekara ta 2025.