Ƙasar Nijar ta saka sunan Shugaba Buhari a wata hanya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Alhamis ne Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Jamhuriyar Nijar ta sanya sunan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wata hanya a ƙasar, wanda a cewar sanarwar alama ce da ke nuna irin mutuntawar da makwafciyar ƙasar ta Nijeriya ke yi masa.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a Yamai, babban birnin ƙasar Nijar, jim kaɗan bayan da Mista Buhari ya ƙaddamar da wata babbar hanya mai sunan sa.

Garba Shehu ya ce Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoun, tare da rakiyar magajin garin Yamai da sauran jami’ai, sun kai wa Buhari rangadin wata babbar hanya mai tsawon kilomita 3.8 wanda aka ƙaddamar da ita bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar.

Hadimin shugaban ƙasar ya ambato Muhammadu Buhari yana nuna jin daɗinsa da alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da makwabtanta.

Buhari ya bayyana imanin cewa irin wannan alaƙar ta taimaka matuƙa, musamman a fannin magance matsalar tsaro a kan iyakokin ƙasar, da shigo da makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma fasa ƙwauri.

Garba Shehu ya ce Buhari ya hau karagar mulki a shekarar 2015, ya buɗe wata tattaunawa mai ƙarfi da ƙasashen Nijar, Benin, Chadi, da Kamaru, lamarin da ya haifar da kyakkyawar alaqa ta diflomasiyya ga ƙasashen biyu.

“Shugaba Buhari yana matuqar mutunta makwabtanmu, kuma ya fahimci ma’anar kyakkyawar makwabtaka.

“Kafin wannan gwamnatin, wasu daga cikin waɗannan ƙasashe sun yi ƙorafin cewa ko shugabannin Nijeriya ba su yi magana da su ba. Mun buɗe tattaunawa da su kuma abin ya ci tura.

“Muna haɗa kai da su kan muhimman al’amura, musamman a fannin tsaro, magance fasa-ƙwauri, da shigo da muggan makamai, don haka haɗin gwiwar ya kammala,” inji Garba Shehu.

Mai taimaka wa shugaban ƙasar ya yi imanin cewa Shugaba Bubari zai bar baya a ranar 29 ga Mayu, 2023, kyakkyawar alaƙa, da aka gina  tsakanin makwabtan Nijeriya, kuma ana sa ran wanda zai gaje shi zai gina shi.

Shugaban na Nijeriya ya ziyarci birnin Yamai ne domin halartar taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU, kan bunƙasa masana’antu da haɓaka tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *