An sako wani malami Ba’amurke, wanda aka yanke wa hukunci bisa kuskure, kuma ake tsare da shi a Rasha, Marc Fogel, a wani abin da fadar White House ta bayyana a matsayin diflomasiyya da ka iya ciyar da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Steve Witkoff, ɗan aike na musamman daga Shugaba Donald Trump, ya bar filin saukar jirage na Rasha tare da Fogel, wani malamin tarihi daga Pennsylɓania, kuma ana sa ran zai sake haɗuwa da iyalinsa a ƙarshen wannan rana.
An kama Fogel a watan Agustan 2021 kuma yana zaman gidan yari na shekaru 14. Iyalinsa da magoya bayansa sun ce yana tafiya ne da marijuana maganin da aka ba shi daga umurnin likita, kuma gwamnatin Shugaba Joe Biden ta ayyana shi a matsayin wanda aka tsare bisa zalunci a watan Disamba.
A cewar mai ba wa Trump shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz, Amurka da Rasha sun “tattaunawa yarjejeniya” don tabbatar da sakin Fogel.
Duk da haka, bai bayyana abin da ɓangaren Rasha zai samu na daga wannan yarjejeniyar daga wurin Amurka ba, duk da cewa, tattaunawar da aka yi a baya sun shafi sakin Rashawa a wasu da Amurka ko ƙawayenta suka kama.
Waltz ya ce, ci gaban ya kasance wata “alama ce da muke tafiya kan hanya madaidaiciya don kawo ƙarshen mummunan yaƙin da ake yi a Ukraine.”
Trump, ɗan jam’iyyar Republican, ya yi alƙawarin samar da hanyar kawo ƙarshen rikicin.
Trump ya kuma yi magana kan samun kyakkyawar alaƙa da shugaban Rasha ɓladimir Putin, wanda ya ƙaddamar da wani gagarumin farmaki a Ukraine shekaru uku da suka wuce. A watan da ya gabata, Trump ya ce gwamnatinsa tana tattaunawa da Rasha kan yaƙin.
‘Yan uwan Fogel sun ce “ba su san da wacce irin kalma ce za su iya yin godiya ba, domin sun samu sauki da kuma gushewar damuwa” da suka ji labarin dawowar sa gida, inda suka ƙara da cewa: “Wannan shi ne lokaci mafi duhu da zafi a rayuwarmu, amma a yau mun fara samun sauki,” inji su. “A karon farko cikin shekaru, danginmu na za su iya kallon gaba cike da kyakkyawar fata.”
Saidai babu wani ƙarin haske daga Moscow game da sakin Fogel a ranar Talata.
Sauran Amurkawa kuma suna ci gaba da zama kurkuku a Rasha, yayin da ba su samu damar shiga cikin wani gagarumin musayar fursunoni da aka yi a watan Agustan da ya gabata wanda ya sa ɗan jarida Wall Street, Eɓan Gershkoɓich shaƙar iskan ‘yanci.
Sannan akwai wata ‘yar asalin ƙasar Amurka da Rasha, Ksenia Khaɓana, wacce aka yankewa hukunci a watan Agusta da laifin cin amanar ƙasa, aka kuma yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru 12 a gidan yari, kan zargin bayar da gudunmawar kimanin dala 52 ga wata ƙungiyar agaji da ke taimaka wa Ukraine.
Fadar White House ta Biden a lokacin ta kira hukuncin da aka yanke a matsayin “zalunci mai tsanani.”