Ƙasar Sa’udiyya ta yi ƙarin kuɗin shiga tasi

Daga AISHA ASAS

Babbar Hukumar kula da sufuri ta Qasar Sa’udiyya ta yi ƙarin kashi 17 bisa ɗari na kuɗin shiga motar haya ta tasi. Hukumar ta bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata.

Hukumar ta ce, mafi ƙarancin cajin kuɗin shiga tasi zai koma Rilay 10 (wanda zai kama 1108.59 a kuɗin Nijeriya) tare kuma da ɗaukar fasinja da ba su wuce huɗu ba.

Wannan sabon farashin na nuni da cewa, ko wanne kilomita ɗaya da fasinja zai yi a motar haya, za a caje shi Riyal 2.1 (232.80 a kuɗin Nijeriya) saɓanin can baya da kilomita ɗaya yake kan farashin 1.8 ( Naira 199.54). Hakan na nuna ƙarin kashi 16.67 cikin ɗari ne aka yi.

Hakazalika shima kuɗin jiran fasinja ya shiga, ya fito, ya ƙaru da kashi 12.5 bisa ɗari, yayin da fasinjan da ya kira tasi gida bai fito da wuri ba, cajinshi ya ƙaru zuwa 0.9(99.77), saɓanin farashin sa na baya da yake 0.8 (Naira 88.69). Wannan shine farashin ko da kuwa motar ba ta yi gudu sosai ba.

A ɓangaren masu buɗe mita don tafiya bisa yarjejeniyar ciniki, su ma hukumar ta sanar da tashin na su farashin zuwa 16.36 bisa ɗari, wanda zai sa ƙarancin kuɗin su zama Riyal 6.4 (709.49 kuɗin Nijeriya), wanda a baya yake Riyal 5.5 (609.71 a kuɗin Nijeriya).

Dangane da tasi mai girma da za ta iya ɗaukar fasinja biyar ko fiye, su ma an sanar da tashin na su farashin da 21.67 bisa ɗari ga masu buɗaɗɗiyar yarjejeniya, wanda zai mayar da farashin na su zuwa Riyal 7.3 ( Naira 809.26), saɓanin inda aka fito da yake Riyal 6 (Naira 665.14).

Shi kuma kuɗin jira na ire-iren waɗannan motoci, za su ƙaru da kashi 22.22 bisa ɗari, hakan zai sa kowanne minti na zaman jiran ya kama 1.1 (121.94), saɓanin sanannen farashin na sa wato Rilay 0.9 (99.77).