Ƙasar Sin ta amsa sunanta na aminiya ta ƙwarai ga ƙasashen Afrika

Daga CMG HAUSA

Har kullum kulawar kasar Sin ga aminanta na Afrika, ya kasance abun burgewa, da ya kamata manyan kasashe irinta su yi koyi da shi. Yadda ake maganar an bar kasashen Afrika a baya idan ana tattauna a dandamalin duniya, kamata ya yi a rika ganin tallafin wadannan manyan kasashe a nahiyar ta Afrika idan har da gaske suke. Ban da kasar Sin, ba ka jin wata kasa dake abubuwan na tallafi masu kwari na a zo a gani, wadanda kuma suka shafi jama’a kai tsaye.

Hausawa kan ce ruwan da ya dake ka, shi ne ruwa. Tabbas haka ne, domin wanda ya ba ka tallafi na zahiri kuma ka amfana, hakika shi ne ya taimake ka kuma ya damu da kai.

Yayin da tsarin kiwon lafiya ke fuskantar matsi a kasashen nahiyar, saboda tarin annoba da ake fama da su, kasar Sin ta yi hobbasa, inda a baya-bayan nan, ofishin jakadancinta dake Uganda da hadin gwiwar wasu kamfanonin kasar da ma tawagar jami’an lafiya dake kasar, suka mikawa asibitin sada zumunta na Sin da Uganda, kayayyakin aiki domin taimakawa kasar a yakin da take da cutar Ebola da kuma ta COVID-19.

Tun cikin 1983 kasar Sin ta fara tura jami’an lafiya da kayayyakin kiwon lafiya zuwa kasar Uganda, wanda kawo yanzu shekaru kusan 40 ke nan, amma ba ta gajiya ba. Wannan kadai ya isa ya kara tabbatarwa jama’ar duniya, musamman wadanda lamarin ya shafa kai tsaye cewa, kasar Sin ta kasance aminiya ta kwarai, kuma abun dagoro.

Baya ga tallafin kayayyakin, kasar Sin za ta taimaka wajen fadada asibitin zuwa cibiyar karbar marasa lafiya na gaggawa kamar haddura da makamantansu, wanda ake ganin ba kasar ce kadai za ta amfana ba, har ma da kasashe makwabta.

Irin wannan tallafi da jama’a ke iya gani tare da amfana da shi kai tsaye, shi ne ke kara kaunar Sin a zukatan jama’ar Afrika, haka kuma ya sa take kara samun karbuwa a kasashensu.

Taimako ko agajin kiwon lafiya, muhimmin abu ne dake nuna cewa Sin ta damu da yanayin da al’ummar Afrika ke ciki, kuma da gaske aniyarta take, na ganin an samu al’umma mai kyakkyawar makoma. Hakika tallafin Sin bai tsaya a fatar baki ba, domin tana yi ana gani, kuma ana cin moriya. Ya kamata kasashe masu kiran kansu manya, su rage surutu, su yi koyi da kasar Sin wajen ganin al’ummar duniya sun samu ci gaba na bai daya.