Ƙasar Sin ta ciri tuta a fannin kyautata rayuwar masu buƙata ta musamman

Daga SAMINU ALHASSAN

Ko shakka babu, mutane masu buƙata ta musamman dake zaune cikin al’ummun duniya, muhimmin bangare ne na jama’ar dake matuƙar buƙatar kulawa, da lura da agaji, kasancewar su mutane da ba za su iya yin wasu abubuwa na buƙatun rayuwa da kan su ba.

Lura da haka ne ya sa hukumomi a matakai daban daban, ke yin kiraye kiraye ga masu ruwa da tsaki, don gane da buƙatar kara lura da buƙatun masu nakasa. Bisa hakan ya sa a nan ƙasar Sin, mahukuntan ƙasar ke gudanar da manufofi daki daki, na shawo kan matsaloli da wannan rukuni na mutane ke fuskanta, musamman cikin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar.

An tanadi irin waɗannan manufofi, cikin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasar Sin karo na 13, wanda ƙasar ta aiwatarwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, inda ƙarƙashin su aka tanadi samar da karin hidimomin gyara dubban gidajen kwana ga masu buƙata ta musamman, da sauran matakan kawar musu da talauci.

Kaza lika ƙasar Sin ta yi rawar gani, wajen aiwatar da gyare-gyare ga manyan ababen more rayuwa da wannan rukuni na al’umma ke buƙata a fannin zirga-zirga, wato yayin da suke tafiye tafiye a titunan mota, da jiragen ƙasa, da na sama da sauran su.

A makarantu ma, an samar da na’urori na zamani dake iya taimaka musu, wajen saukakawa koyo da koyarwa. Har da ma fannin amfani da yanar gizo domin raya sana’o’i, ko saye da sayarwa, da ma samun nishadi. Kaza lika suna samun hidimomi na kula da tsofaffi masu buƙata ta musamman, baya ga fannin wasanni, wanda a shekarun baya bayan nan, ƙasar Sin ke kara samun tagomashi a ɓangaren raya wasannin ajin masu buƙatar musamman.

Bisa waɗannan dalilai da ma wasu, muna iya ganin yadda gwamnatin ƙasar Sin ta yi namijin ƙoƙari, wajen ƙara inganta rayuwar masu buƙatar musamman, ta yadda za su samu damar yin kyakkyawar rayuwa, kamar dai yadda burin mahukuntan kasar yake, cewa ba za a bar kowa a baya ba, yayin da ake aiwatar da muhimman manufofin kyautata rayuwar al’umma.

Fassarawa: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *